Uncategorized
‘Yan Makarantan Jami’ar Kwaleji Fiye da 6, a Jihar Sokoto sun Mutu a wata Hadarin Mota
Naija News Hausa ta karbi rahoto da cewa wasu ‘yan Makarantan Kwalejin ‘Sokoto State College of Education’ hade da wasu mutane biyar sun rasa rayukan su a wata hadarin mota da ya faru a hanyar da ta bi Maiyama zuwa Jega, a Jihar Kebbi.
Bisa ga bayanin wani da ya gana da hadarin, Ya bayyana da cewa Motar Toyota Tercel da ke dauke da ‘yan makarantan daga garin Kotongora, Jihar Neja ya hade ne da wata Tirela a yayin da suka kusanci Maiyama, wata gari da ke a Jihar Kebbi.
An bayyana da cewa mutane shidda daga cikin Motar Toyotar ne suka mutu anan take da hadarin ya faru, sa’anan wasu biyu kuma suka mutu a baya a lokacin da aka kai su Ofishin Jami’an tsaron yankin.
Wata Kyakyawar yarinya da ke cikin motar da ke da alamar rayuwa, ita ma ta mutu ne bisa an kai ta ga Asibitin Janara ta Jega, a yayin da ake kokarin kai ta ga babban Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke a Birnin Kebbi.
Abin kaito, wani mutumin da matar sa ta mutu a yayin da take bakin haifuwa, shima ya mutu a hadarin.
Bisa bayanin da aka bayar ga manema labarai, mutumin ya kama hanyar birnin Kebbi ne don ya je jinyar matarsa da ta mutu, sai shima ya cinma karshen rayuwa.
Ita kuma ‘yar kyakyawar yarinyar da ta mutu, an bayyana da cewa tana dawowa ne daga garin Ilorin wajen Auren yayanta sai ta cinma karshen rai.
“Ya kamata ne a ce shekaran nan ne zata karshe karatun ta, amma sai ga mai rana ya iso” inji mai bada labarin ga Menama labarai.
Karanta wannan kuma: ‘Yan Sanda sun Kame Hassana da ta saka Guba cikin abincin Mijinta