Labaran Najeriya
A Karshe, Buhari ya Rattaba hannu ga biyan Kankanin Albashin Ma’aikata na naira 30,000
0:00 / 0:00
Bayan jayayya da jita-jita hade da barazanar Ma’aikatan kasa game da kankanin albashi na naira dubu 30,000 da gidan Majalisai suka gabatar a baya, kamar yadda muka kuma sanar a wata sanarwa a Naija News Hausa.
Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ga amincewa da kuma rattaba hannun sa da takardan dokan biyan kankanin albashin ma’aikata na naira dubu Talatin, kamar yadda aka aminta a baya.
Wanda ya biyo ne bayan da Gidan Majalisar Dattijai da Majalisar Wakilai suka amince da dokar da kuma sanya hannun su a kwanakin baya.
Naija News Hausa ta gane da cewa Ma’aikata a baya sun kara tunawa da kuma rokon shugaba Muhammadu Buhari da yin hanzari wajen rattaba hannu ga dokar kamin ranar 1 ga watan Mayu 2019, a yadda shugabancin kasar ta so a da.
© 2025 Naija News, a division of Polance Media Inc.