Connect with us

Labaran Najeriya

Kalli abinda Goodluck Jonathan ya gayawa Reno Omokri game da shugaba Buhari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Tsohon Shugaban Kasan Najeriya, Goodluck Jonathan ya gargadi tsohon ma’ikacinsa, Reno Omokri da ya nuna halin girmamawa da kirki ga shugaba Muhammadu Buhari.

Naija News Hausa ta gane da wannan hirar ne a wata sakon da Omokri da kansa ya rabar a layin nishadarwa ta Twitter na sa, a maraicen ranar Litini da ta gabata.

A bayanin Omokri, Ya ce “Ban taba ganin mutumin irin Jonathan ba, Ban san yadda Allah yayi Jonathan ba da irin halin kirki da ban girma.”

“Banyi zaton cewa shugaba Muhammadu Buhari zai iya gabatar ko nuna irin wannan halin ba ga tsohon shuga Jonathan ko kuma ga Ibrahim Babangida, tsohon shugaban kasar.”

Omokri ya bayyana da cewa ya karbi kira daga tsohon shugaban kasa, “Ban taba haduwa da Fasto, Liman ko wani Fafaroma ba da irin wannan halin girmamawa irin ta Goodluck Jonathan.” inji Reno.

“Jonathan ya kira ni akan wayan Salula da bukata na da kara bada girma da kuma nuna halin kirki ga shugaba Muhammadu Buhari [@MBuhari], Ban yi zata ko tsanmanin Buhari zai iya bayyana irin hakan ba” inji Reno.

“Buhari yay iya gabatar da hakan ga Jonathan, IBB ko Obasanjo kuwa?”

Kalli sakon kamar yadda Reno ya aika a layin Twitter;

Naija News Hausa ta tuna a baya da cewa Reno Omokri ya bada Tallafin Mota ga duk wadanda suka bada kansu don koma Jihar su da yankunan su a kwanakin baya da aka daga ranar hidimar zaben shugaban kasa.

Karanta wannan kuma:  Shugabancin Buhari ba ta da wata Unfani ga kasar Najeriya – Ango Abdullahi