Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 26 ga Watan Afrilu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 26 ga Watan Afrilu, 2019

1. Majalisar Dattijai sun yi kira ga IGP akan Matsalar tsaro a kasar Najeriya

Gidan Majalisar Dattijan Najeriya sun aika kira ga shugaban Jami’an tsaron ‘yan sandan kasar, IGP Mohammed Adamu, don ya yi bayani ga gidan majalisar akan yanayin matsalar tsaro da ke gudana a kasar.

Naija News ta gane da cewa IGP zai bayyana ga Majalisar ne irin matakin da ‘yan sandan kasar ke shirye da shi don magance matsalar tsaro da ake ciki a Najeriya.

2. Hukumar FEC zata yi Hidimar zaman Sai wata Rana a ranar 22 ga watan Mayu

Gwamnatin Tarayya ta sanar daga bakin Ministan Yadarwa da Al’adun kasa, Alhaji Lai Mohammed, da cewa Kungiyar Kwamitin Tarayya (FEC) zasu gudanar da hidimar Sai Wata Sa’a a ranar 22 ga watan Mayu ta shekarar 2019.

An sanar da hakan ne bayan ganawar da hukumar ta yi da da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, a ranar Alhamis da ta gabata a birnin Abuja, babban birnin Tarayyar kasar Najeriya.

3. Shugaba Muhammadu Buhari yayi Ziyarar Kai Tsaye zuwa kasar UK

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari zai yi tsawon kwanaki Goma shadaya a ziyarar kai tsaye da ya yi zuwa kasar UK ranar Alhamis da ta gabata.

Naija News Hausa ta gane da cewa kasar UK ta zama daya daga cikin kasashen da shugaban ke kai ziyarar kai-da-kai tun a shekarar 2015 da ya hau kan mulkin Najeriya.

4. Atiku na batun gabatar da karar Shugaban Hukumar INEC hade da wasu

Naija News Hausa ta gane da wata alamar da ya nuna da watakilar cewa dan takaran kujerar shugaban kasa daga Jam’iyyar PDP a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar zai yi karar shugaban hukumar gudanar da hidimar zaben kasar (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu.

Ka tuna da cewa Atiku yayi zargin Hukumar INEC da cewa sun kadamar da makirci ga hidimar zaben 2019, musanman na gabatar da Muhammadu Buhari a matsayin mai nasara ga zaben kasar.

5. IGP ya bada umarni aiki akan duti na tsawon awowi Takwas ga Jami’an tsaro

Shugaban Jami’an tsaron ‘yan sandan kasar Najeriya, Ag IGP Mohammed Adamu ya bada sabuwar umarni na mayar da tsayin kan aiki na tsawon awowi 8 ga jami’an tsaro.

IGP ya gabatar da wannan sabon dokar ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu da ta gabata a wata ganawa da aka yi a birnin Abuja.

6. Sanatoci sun gabatar da sabuwar zargi akan matsalar tsaron da Najeriya ke ciki

A wata zama da Sanatocin kasar Najeriya suka yi a ranar Alhamis da ta wuce, sun gabatar da zargin cewa akwai hadin kan wasu ‘yan siyasa, ‘yan sanda da sojojin Najeriya akan kashe-kashen da harin da ‘yan ta’adda ke yi a kasar, musanman a Arewacin kasar.

“Kashe-kashe da hare-hare a kasar Najeriya ya zama kamar sana’a a halin da ake ciki a yau” inji Sanatocin.

7. Kotu na aiki da Dokar Zabe ne, ba da bidiyon kan Layin Nishadarwa ba – Keyamo

Mista Festus Keyamo, Kakakin yada yawun Jam’iyyar APC ga hidimar yakin neman zabe, ya bayyana da cewa bidiyon da ke mamaye yanar gizo da zargin cewa an kadamar da makirci ga zaben shugaban kasa a shekarar 2019 ba ta da wata amfani fiye da dokar hukumar zabe da Kotu zata yi amfani da ita.

Ka tuna da cewa Jam’iyyar PDP sun gabatar da rashin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa ta shekarar 2019 akan cewa an kadamar da makirci a hidimar.

8. Sarkin Kano ya nada wani dan China a matsayin Wakili a Jihar

Naija News Hausa ta gano da wata bidiyon da ke dauke da masana’anci dan China mai suna ‘Mike Zhang’ sanye da rawani.

Mike Zhang ya samun sabon sauratan ne a yayin da Mai Martaba, Sarki Muhammad Sanusi II, Sarkin Kano ya nada shi a matsayin wakilin ‘yan Chana da ke a Jihar Kano.

Ka samu kari da cikakken labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com