Connect with us

Uncategorized

Sojojin Najeriya sun kame masu Kira da Samar da Makami ga ‘yan Ta’adda a Kontagora (Neja) da Katsina

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rukunin Rundunar Sojojin Najeriya ta “Operation Harbin Kunama III” sun sanar da cin nasara da kame wani mai samar da Makamai ga ‘yan hari da makami a shiyar Jibia da Batsari, Jihar Katsina.

A wata sanarwa da aka bayar daga bakin kakakin yada yawun rundunar sojojin Najeriya, Colonel Sagir Musa, ya bayyana da cewa sun kame wani mai kirar mugayen makamai, Marwana Abubakar a shiyar Kwashabawa, a karamar hukumar Jibia ta Jihar Katsina, a ranar Laraba, 8 ga watan Mayu da ta gabata.

Ya kara bayyana da cewa sun karbi likin wasu kuma a garin Kontagora ta Jihar Neja.

“Rundunar Sojojin sun gane da wani wuri a garin Kontagora ta Jihar Neja, inda sojoji suka kame wani mai suna Salisu Ibrahim da aka gane da kirar muggan makamai.”

Col. Sagir ya bayyana da cewa lallai sojojin sun katange wani mai suna Salisu Ibrahim, da suka gane bayan bincike da kirar makamai a garin Kontagora, karamar hukuma a Jihar Neja.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Sojojin Najeriya sun Katange rukunin ‘Yan Ta’adda a Kaduna