Connect with us

Manyan labarai daga jaridun Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 14 ga Watan Mayu, Shekara ta 2019

Published

on

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 14 ga Watan Mayu, 2019

1. Gwamna Samuel Ortom ya gana da shugaba Muhammadu Buhari

A yau safiyar Talata, 14 ga watan Mayu, Shugaba Muhammadu Buhari yayi ganawar kofa kulle da Gwamnan Jihar Legas, Akinwunmi Ambode; Gwamnan Jihar Benue, Samuel Ortom da kuma Nasir El-Rufai, Gwamnan Jihar Kaduna, a nan cikin fadar shugaban kasa ta Birnin Abuja.

Anan ne Gwamna Ortom ya bayyana yanayi da mawuyacin hali da Jihar Benue ke a ciki ga shugaba Buhari.

2. Ganduje ya Mika Sandar Ikon Sarauta ga Sabbin Sarakan Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, a ranar Litini da ta gabata, ya bayar da Sandar Ikon Sarauta ga sabbin Sarakai Hudu da ya nada a Jihar Kano.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa Gwamna Ganduje ya rabar da kujerar Sarautan Jihar Kano ga rukuni Biyar hade da wadda Muhammadu Sanusi ke jagoranta a da.

3. IGP ya nada sabon Ofisan karban ƙara

Shugaban Jami’an Tsaron ‘Yan Sandan Najeriya, IGP Muhammed Adamu, ya nada ACP Markus Ishaku Basiran a matsayin Ofisan da zai jagoranci rukunin karban kara, (Complaints Response Unit – CRU).

Yin hakan, ACP Markus Ishaku Basiran ya maye gurbin ACP Abayomi Shogunle, wanda aka mayar a matsayin sabon Area Kwamanda na yankin Nkalangi, a Jihar Ebonyi.

4. Za a Rantsar da Shugaba Buhari a hidimar lape ranar 29 ga watan Mayu

Shugabancin kasar Najeriya ta gabatar cewa za a rantsar da shugaba Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasan Najeriya a karo ta biyu, ranar 29 ga watan Mayu 2019.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa hidimar zai kasance ne a lape, ba kamar yadda aka saba yi ba.

5. An tsige Sowore daga kujerar shugabancin Jam’iyyar AAC

Jam’iyyar Siyasa ta African Action Congress (AAC) sun gabatar da dakatar da Omoyele Sowore a matsayin Ciyaman na Tarayyar Jam’iyyar, hade da wasu kuma daga Jam’iyyar.

Naija News ta gane da hakan ne a wata sanarwa da Ciyaman na Kwamitin Jam’iyyar ya bayar a ranar Litini, 13 ga watan Mayu, 2019 a birnin Abuja.

6. “Na Karu ga Fahimta da Fasaha a yanzu” inji Ambode bayan da ya ziyarci Shugaba Buhari

Gwamnan Jihar Legas, Gwamna Akinwunmi Ambode, a wata ziyarar da yayi ga shugaba Muhammadu Buhari ranar Litini da ta wuce, ya bayyana cewa ya karu da fahimtar lamarin siyasa a shekaru hudu da yayi a kujerar shugabancin sa a Jihar Legas.

Ambode ya fadi hakan ne a wata ziyarar da ya kai ga Fadar shugaban kasa, anan birnin Abuja don nuna godiya ga goyon baya.

7. Ba zani sake neman zabe ba bayan shekarar 2023 – Ekweremadu

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ike Ekweremadu ya bayyana da cewa ba zai kara neman takara a gidan Majalisa ba idan ya gama wakilcin shi a shekarar 2023.

Ya bayyana hakan ne ga manema labarai a ranar 12 ga watan Mayu, a wajen hidimar murnan ranar haifuwa da cika shekaru 57 da yayi.

8. Dalilin da ya sa Hukumar EFCC ke binciken Saraki – Sagay

Ciyaman na Kwamitin Shawarwari ga shugaban Kasa, Farfesa Itse Sagay, ya bayyana da cewa Hukumar EFCC na binciken Bukola Saraki ne akan wasu tarin dukiya da yayi a hanyar da bata dace ba.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa EFCC, a makon da ta gabata sun dakile gida da dukiyar Sanata Saraki da ke a shiyar Ikoyi, a Jihar Legas.

Ka samu kari da cikakken labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com