Uncategorized
Kalli Tsarin Sabbin Sarakai Biyar da zasu Wakilci Kananan Hukumomin Jihar Kano
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya gabatar da kara Kujerar Sarauta Biyar (5) a Jihar Kano.
Kamar yadda muka sanar a wannan gidan labarai ta Naija News Hausa cewa Gidan Majalisar Dokokin Jihar Kano da Kwamitin Sauratan Jihar sun amince da karin kujerar Sarauta a Jihar Kano ne don ganin cewa hakan zai taimaka wajen samar da ayuka, rage jayayya, da kuma magance wasu rikice-rikicen dake tasowa a Jihar tsakanin al’umma.
Ga Yadda Aka Rabar da Kananan Hukumomin Kano
1- Kano Emirate:
Kano Emirate a karkashin jagorancin mai Martaba, Muhammadu Sanusi, Sarkin Tarayyar Kano zai wakilci kananan hukumomi Goma (10). Gasu nan a kasa;
- Kano Municipal
- Tarauni
- Dala
- Nassarawa
- Fagge
- Gwale
- Kumbotso
- Ungogo
- Dawakin Kudu, da
- Minjibir
2- Rano Emirates:
Mai Sarautan Rano zai yi sauratan kananan hukumomi goma shima.
- Rano
- Bunkure
- Kibiya
- Takai
- Sumaila
- Kura
- Doguwa
- Tudun Wada
- Kiru
- Bebeji.
3- Gaya Emirate
Mai Sarautan Gaya Emirate zai shugabanci kananan hukumomi Takwas (8)
- Gaya
- Ajingi
- Albasu
- Wudil
- Garko
- Warawa
- Gezawa
- Gabasawa
4- Karaye Emirate:
Mai Sauratan Karaye Emirate shima na da hakin jagorancin kananan hukumomi Shidda (6)
- Karaye
- Rogo
- Gwarzo
- Kabo Rimin Gado
- Madobi
- Garun Malam
5- Bichi Emirate:
Sarkin Bichi Emirate shima zai wakilci kananan hukumomi Tara (9)
- Bichi
- Bagwai
- Shanono
- Tsanyawa
- Kunchi
- Makoda
- Danbatta
- Dawakin Tofa
- Tofa
Naija News Hausa na da sanin cewa Jihar Kano na da kananan hukumomi 44 a karkashin ta, an kuwa rabar da dukan su a karkashin jagorancin Sarakai Biyar hade da Mai Martaba, Muhammadu Sanusi.