Connect with us

Labaran Najeriya

#KanoEmirate: Gwamna Ganduje ya bayar da Miliyan N6m, kowane ga Zainab Aliyu da Ibrahim

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayar da kyautar kudi Naira Miliyan  Goma Shabiyu (N12 million), Miliyan Shidda ga Zainab Aliyu, Miliyan Shidda kuma ga Ibrahim Abubakar da aka sako daga kasar Saudi Arabia bayan kame su da aka yi a kan zargin daukar mugan kwayoyi.

Naija News Hausa ta fahimta da hakan ne bisa wata sanarwa da Gwamna Ganduje ya bayar da kansa a Jihar Kano.

Ganduje ya gabatar da bayar da kudin ne a wata taro, inda ya karbi marabtan Wakilai daga Gwamnatin Tarayyar Najeriya hade da Mataimakin musanman ga Shugaba Buhari ga lamarin kasar waje, Abike Dabiri-Erewa, a Gidan Gwamnatin Jihar Kano.

Ziyarar wakilan a Jihar Kano ya kasance ne don mikar da Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar ga Gwamnatin Kano, bayan da Gwamnatin Tarayyar kasar Najeriya ta nemi yancin su daga hannun kasar Saudi Arabia.

Ganin hakan ne ‎Ganduje ya nuna tausayawa ga Zainab da Ibrahim, ya kuma tallafa masu da bayar ga kowanen su Miliyan Shida (N6m).

Naija News ta sanar a wata labarai a baya cewa Hukumar Saudi Arabia sun kame ‘yar Najeriya, Zainab Aliyu, da zargin kama ta da mugan kwayoyin da dokar kasar bata amince da ita ba, aka kuma tsare ta da Ibrahim daga zuwa hidimar su ta Umrah.

KARANTA WANNAN KUMA;  ‘Yar Makarantar Dapchi, Leah Sharibu, da Boko Haram suka sace a baya ta kai ga shekara 16 ga haifuwa, duk a kangin Boko Haram