Labaran Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari ya Ziyarci Saudi Arabia don Hidimar Umrah
Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi gayyatar Sarki Salman Bin Abdulaziz, da ke jagorancin Saudi Arabia da kuma wakilcin Manyan Masallacin Saudi Arabia biyu, don kadamar da hidimar Umrah a kasar.
Naija News Hausa ta gane da tafiyar shugaban ne bisa sanarwan da Bashir Ahmed, mai wakilcin shugaba Buhari wajen sadarwa ya bayar a ranar a yau Alhamis, 16 da Watan Mayu.
Kalli Sanarwan a Kasa a layin Twitter;
President @MBuhari has accepted the invitation of @KingSalman Bin Abdulaziz, the ruler of Saudi Arabia and Custodian of the Two Holy Mosques to perform the Umrah in the Kingdom.
The President will embark on the journey May 16th, and will be accompanied by close personal aides. pic.twitter.com/nFRTwYjzKt
— Bashir Ahmad (@BashirAhmaad) May 15, 2019
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wata gargadi mai karfin gaske ga Shahararrun ‘yan wasan Kwaikwayo da Ban Dariya na Najeriya, cewa su janye daga yi masa ba’a wajen hidimar su.
“Ku bar yin ba’a da ni, sauran kasashen waje na da tasu matsalar da suke fuskanta a kasar su. Amma ba zaku taba gan suna yin ba’a ga shugabanan su ba” inji Buhari.