Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 28 ga Watan Mayu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Manyan Labaran Jaridun Najeriya a Yau

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 28 ga Watan Mayu, 2019

1. Gwamnatin Tarayya ta gabatar da ranar 29 ga Mayu a matsayin ranar Hutu

Gwamnatin Tarayyar Najeriya a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta gabatar da ranar Laraba, 29 ga Mayu a matsayin ranar Hutu ga ma’aikata da ‘yan makaranta don hidimar rantsar da shugaban kasa a shekarar 2019 ga shugabanci ta karo biyu.

Naija News ta gane da rahoton ne bisa sanarwan da Ministan Harkokin Kasa, Janar Abdulrahman Dambazau (rtd) ya bayar a wakilcin Gwamnatin Tarayya, a ranar 27 ga watan Mayu da ta gabata.

2. Kina yada yawun ki ba tare da cikakken sani ba, Gwamnatin Tarayya ta mayar da martani ga Aisha Buhari

Babban Mataimakin shugaban kasa a harkokin zuba Jaruka, Maryam Uwais ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ba ta kasa ba a hidimar ta na Social Investment Programmes (SIP).

Uwais ta fadi hakan ne don mayar da yawu ga zancen matan shugaban kasar, Aishsa Buhari, wada ta fada a baya cewa gwamnatin kasar ta kasa a harkokin zuba jaruka, musanman a Arewacin kasar.

3. Kotu ta Tsige dan gidan Majalisar Wakilai a APC na Jihar Imo, ta kuma gabatar da sabin dan Majalisa

Kotun Koli ta birnin Owerri a ranar Litini da ta wuce ta bada umarni ga Hukumar Gudanar da Himadar Zaben Kasar (INEC) da bayar da Takardan yancin shugabanci ga dan takara daga PDP ga kujerar gidan majalisar wakilan Jihar Imo, Mista Kingsley Echendu, don wakilcin yankin Nkwerre/Nwangele/Njaba/Isu a majalisar Jihar.

Wannan ya biyo ne bayan da Kotun ta tsige Hon. Ugonna Ozurigbo, dan takara daga Jam’iyyar APC akan wata kula.

4. INEC ta bayar da Takardan Yancin shugabanci ga mai nasara ga kujerar Gwamnan Jihar Zamfara

A ranar Litini da ta wuce, hukumar INEC ta Jihar Zamfara ta mika takardan yancin shugabancin Jihar ga mai nasara da kuma dace wa ga kujerar Gwamnan Jihar, bisa dokar zaben kasar.

Wannan matakin ya biyo ne bayan da kotun a ranar Jumm’a da ta wuce ta gabatar da tsige wanda a da aka bayar a matsayin mai nasara ga zaben.

5. Shugaba Buhari ya karbi takardan gabatar da Asusun sa

A ranar Litini, 27 ga watan Mayu da ta wuce, shugaba Muhammadu Buhari ya karbi takardan da ake cikawa na gabatar da asusun dan siyasa ko ma’aikaci a kasar, daga hannun Ciyaman na Hukumar CCB, Farfesa Muhammad Isa.

Naija News Hausa ta fahimta da hakan ne a sanarwan da aka bayar daga Bashir Ahmed, mataimaki ga shugaba Buhari ga hidimar sadarwa a layin yanar gizon nishadi.

6. Shugabancin kasa ta yi bayyani game da dakatar da ‘yan ta’addan Boko Haram

Garba Shehu, babban mataimakin shugaba Muhammadu Buhari a lamarin sanarwa ga layin yanar gizo, ya bayyana da cewa zai zama da wuya gwamnatin kasar ta iya dakatar da ta’addancin Boko Haram a Najeriya.

Mista Shehu ya bayyana hakan ne a wata gabatarwa da yayi da gidan talabijin na Channels Television da kuma Sunrise daily.

7. Abinda Gwamnonin Arewa suka gayawa shugaba Buhari a Aso Rock

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Gwamnonin Arewacin Najeriya a ranar Litini da ta gabata sun zi zaman tattaunawa na kofa kulle da shugaba Muhammadu Buhari, a fadar shugaban kasa don tattaunawa akan yadda za a dakatar da kashe-kashe da hare-haren ‘yan ta’adda a Jihohin.

Zaman ta karbi halartan Gwamnonin Arewa 10 cikin 19 da kasar ke da ita.

8. Shugaba Muhammadu Buhari ya Rattaba Hannu ga Kasafin Kudin Najeriya

A ranar Litini, 27 ga watan Mayu, Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu ga takardan dokan kasafin kudin Najeriya ta naira Tiriliyan N8.91 na shekarar 2019, a birnin Abuja.

Ka tuna da cewa a watan Disamba ta shekarar 2018 da ya gabata, Shugaba Muhammadu Buhari ya shirya kasafin kudi na naira Tiriliyan N8.83 don gabatar da shi, ko da shike, saboda hidimar Kiristimati da sabuwar shekara, Buhari bai samu ya gabatar da shi ba sai ga watan Afrilu da ta wuce.

9. Na kusa da zama shugaban kasar Najeriya – Okorocha

Tsohon Gwamnan Jiahr Imo, Rochas Okorocha ya rantse da cewa nan gaba zai zama shugaban kasar Najeriya.

Okorocha ya bayyana hakan ne a hidimar ban kwana da yayi a ranar Lahadi da ta gabata a gidan Gwamnatin Tarayyar Jihar Imo da ke a Owerri.

Ka samu kari da cikakken Labaran kasar Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com