Uncategorized
Hukumar EFCC sun kame Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Okorocha da Matarsa
0:00 / 0:00
Naija News Hausa ta karbi rahoto da cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da kuma Kare Tattalin Arzikin Najeriya (EFCC) ta kame Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, hade da matarsa Nkechi Okorocha.
Bisa bayanarwar rahotonnai, Hukumar sun kame shi ne da kuma wasu ‘yan uwan sa da ke zama da shi, Gerald Okorocha, Okey Okorocha, aka kuma katange babban makarantar Jami’a ta Eastern Palm University da yake da ita a Ogboko, Jihar Imo.
Ko da shike a lokacin da aka bayar da wannan rahoton, Naija News Hausa ba ta samu gane da wata bayani ba game da kame Okorocha daga bakin shugaban Hukumar EFCC ko wani ma’aikaci da Ofishin su.
Zamu sanar a layin Hausa.NaijaNews.Com idan mun samu tabbaci ko karin bayani da rahoton.
© 2025 Naija News, a division of Polance Media Inc.