Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 30 ga Watan Mayu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Manyan Labaran Jaridun Najeriya a Yau

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 30 ga Watan Mayu, 2019

1. An Rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari a karo ta biyu ga shugabancin kasa

A ranar Laraba, 29 ga Mayu 2019 da ta gabata, shugaba Muhammadu Buhari yayi rantsuwar jagoranci da daukar alkawalan shugabancin kasar Najeriya a karo ta biyu ga mulkin farar fula.

Buhari yayi rantsuwar ne don bayyana shirin jagorancin kasar Najeriya da dukan ransa da kuma hankalin sa.

2. Obasanjo tare da wasu mutane sun kuri hadarin Jirgin Sama

Naija News ta karbi rahoto da cewa tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, a ranar Laraba da ta wuce ya kuri hadarin jirgin sama hade da wasu.

A fahimtar gidan labaran nan ta mu, wannan itace karo ta biyu da Obasanjo da wasu manya a kasar ke kaurace wa hidimar rantsar da shugaba Muhammadu Buhari.

3. Gobarar Mota ya dauke rayukan a birnin Legas

Akalla mutane biyar suka samu mugun rauni a wata hadarin fashewar motoci da gobara a babban hanyar Legas zuwa Ibadan.

Naija News ta samu rahoto da cewa hadarin ta karshe ya faru ne tsakanin Motar Mercedes Benz da motar Tanki biyu dauke da Man Fetur.

4. Seyi Makinde ya gabatar da Ilimin Kyauta a Jihar Oyo

Sabon Gwamnan Jihar Oyo, Gwamna Seyi Makinde, a ranar Laraba, 29 ga Mayu da ta gabata, ya gabatar da Ilimin Kyauta ga Makarantu Firamare da Sakandiri ta Gwamnati a Jihar.

A hakan ne kuma Gwamna ya bada umarnin cewa a dakatar da biyan kudin Kadamar da Cigaba (Development Levy) a makarantun Firamare da Sakandiri a Jihar.

5. Sarkin Kano, Sanusi ya kauracewa wa hidimar Rantsar da Ganduje

Mai Martaba Sarkin Kano, Mohammadu Sanusi II ya kauracewa hidimar rantsar da Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, duk da kira da aka aika masa kamin hidimar.

Naija News Hausa na da fahimtar cewa aka dan matsala tsakanin su biyun, musanman yadda Ganduje ya rabar da kujerar Sauratan Jihar Kano a kwanakin da suka gabata.

6. Shugaba Muhammadu Buhari ya ki bada gabatarwa a hidimar rantsar da shi

A ranar Laraba, 29 ga watan Mayu 2019, shugaba Muhammadu Buhari yayi rantsuwar shiga Ofishin shugabancin kasar Najeriya a karo ta biyu.

Naija News Hausa na da ganewar cewa Buhari ya yi rantsuwar ne bayan da mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo yayi nashi rantsuwa a missalin karfe 10:30 na safiyar ranar Laraba a Filin Wasan Kwallon kafa ta Abuja, babban birnin Tarayyar kasar Najeriya.

7. Bayanin Goodluck Jonathan game da Rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari

Tsohon Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan yayi gargadi ga ‘yan Najeriya a wata bayani da ya bayar bayan da aka rantsar da shugaba Muhammadu Buhari a shugabancin kasar Najeriya, a karo ta biyu.

“Kada ku cika da damuwa, Dimokradiya ta tabbata hanya daya ta ci gaba da shugabancin kwarai a kasar Najeriya” inji Jonathan.

8. An kunyatar da Oshiomhole a hidimar rantsar da Shugaba Buhari

An yi dirama kadan a ranar jiya Laraba, 29 ga watan Mayu a hidimar rantsar da shugaba Muhammadu Buhari, a yayin da aka kunyatar da Ciyaman na Tarayyar Jam’iyyar APC, Kamrade Adams Oshiomhole.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa Oshiomhole ya tsaya ne a tsakar Babban Alkalin Kotun Najeriya, Ibrahim Tanko Muhammad (CJN) da Manyan Jami’an tsaron kasar.

Yana kan layin ne aka fitar da shi daga kan layin a yayin da ake cikin hidimar.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com