Connect with us

Labaran Najeriya

Arewa Ku Manta da zancen neman Shugabanci a 2023 – inji Shehu Sani

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Sanatan da ya wakilci Jihar Kaduna a Majalisar Dattajai na takwas, Sanata Shehu Sani yayi kira da gargadin Arewa da su manta da zancen neman shugabancin kasar Najeriya daga Arewacin kasar a zaben shugaban kasa ta 2023 da ke a gaba.

“Ku manta da batun neman wanda zai maye gurbin shugaba Muhammadu Buhari a shugabancin Najeriya a zaben shugaban kasa ta 2023” inji shi.

Naija News Hausa ta samu sanin cewa Sanata Shehu Sani yayi wannan bayanin ne a garin Minna, babban birnin Jihar Neja, inda ya fada da cewa lallai Arewa ta lashe kashinta a shugabanci shugaba Muhammadu Buhari.

Sani ya kara da cewa bai dace ba a fara zancen neman shugabanci ba a Arewa, musanman zancen wanda zai maye gurbin Buhari a shugabanci bayan ya sauka.

“Abinda ya daura danko kasar Najeriya itace adalci da halin gaskiya. duk wani mai neman cewa shugabanci ta ci gaba a Arewacin kasar bayan Buhari lallai irin wannan mutumin na neman tashin hankali ne kawai a kasar” inji shi.

“Ya kamata mu gane da cewa ba cin zabe ne zumuncin kasa ba, amma yadda za a kasance da dayantaka da tabbatar da gudanarwa a kowace yanki”