Connect with us

Uncategorized

Jami’an Tsaro sun kame wani Soja mai sayar da Makami ga ‘Yan Fashi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

An kama wani jami’in Sojan Najeriya mai shekaru 32 da zargin sayar da bindigogi ga ‘yan fashi da mahara da ke kai hare-hare a jihar Kaduna sun tsawon shekarun baya.

Naija News Hausa ta samu tabbacin hakan ne bayan da rukunin ‘yan sandan jihar Kaduna suka sanar da kame dakarun soja mai shekarun haifuwa 32, da igiyar Lance Corporal, Koza Yabiliok, da zargin sayar da mugan makamai ga masu sace-sacen mutane a Jihar.

Haka kazalika hukumar ta sanar da kama mutane 61 da ake tuhuma da laifuffuka mai kamanin hakan a fadin Jihar, a makonni biyu da suka gabata.

Lance Corporal Yabiliok yana aikin tsaro ne a daya daga cikin rukunin sojojin ta Jaji Military Cantonment, Jihar Kaduna, ya shaida wa manema labaru yayin da ‘yan sandan ke fadada shi, da cewa ya sayar da kowane bindiga ne a naira N400.

Ya ce ya sayar da makaman ne ga abokin cin mushensa ba da sanin cewa dan fashi ne ba “Ya gaya mini cewa yana buƙatar makamai ne domin kariya ga shanayansa daga masu sata. Dalili kenan da na na sayar da makaman a gare shi. Ban san cewa shi dan fashi ne ba”

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar, Ali Aji Janga, a yayin da yake jawabi, ya bayyana cewa sun kara kamun wasu mutane 62 da ake zargi da laifin aikata irin wannan mugun halin, kamarsu, sace-sace, fashi da makami, da kisan kai da kuma sace-sacen shanaye dadai sauransu.

Ko da shike, ya bayyana cewa hukumar su na kan bincike ga ‘yan fashin, “za a haura dasu a gaban Kotu don hukunci bayan bincike” inji shi.