Labaran Najeriya
Ka kama Obasanjo yanzun nan, Miyetti Allah sun gayawa shugaba Buhari
Kungiyar Makiyaya da aka fi sani da Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), ta gargadi shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnatin Tarayya da kama tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo akan zargin da yake da makiyaya Fulani.
Naija News Hausa ta fahimta da cewa kungiyar sun bayyana hakan ne a yayin da suke mayar da martani game da wata wasika da Obasanjo ya wallafa ga shugaba Muhammadu Buhari ranar Litini, 15 ga watan Yuli da ta gabata, akan yanayin matsalar rashin tsaro ke ake fuskanta a kasar Najeriya.
Naija News ta ruwaito a baya da cewa Obasanjo a cikin wasikar da ya aika ga Buhari, ya bukaci shugabancin sa da daukar matakin musanman akan magance matsalar tsaro da ake fuskanta a kasar.
Bayan hakan, Alhassan Saleh, magatakardan kungiyar Miyetti Allah ya kalubalanci tsohon shugaban kasar, Obasanjo, da kasancewa da halin yarantaka, musanman akan yadda ya ke zargin makiyaya Fulani da ta’addanci a kasar.
“ko da shike akwai matsalar tsaro a kasar, amma banyi tsamanin cewa Fulani ne ke da alhakin hakan ba. saboda hakan, fadin cewa Fulani ne ke da alhakin hakan ya isa da kafa tashin hankali a jihohin kasar.”
“Kwaram da duk wata mugun hari ya faru, ko kamin a gabatar da bincike sai kawai an ambaci makiyaya Fulani. Makiyaya an sansu ne da kiwon shanaye, amma idan har an gane mutum da mugun hali ya kuwa dace a hukunta shi bisa laifin sa”
“Amma, idan har Obasanjo, da karan kansa bayan da ya shugabanci kasar Najeriya da tsawon shekaru da suka shige zai iya fadi da bayyana da wannan zancen, lallai ya kamata a kama shi da kuma hukunta shi a bisa doka. Saboda a bisa gani na bai da wata manufa ta kwarai ga kasar” inji Saleh.
KARANTA WANNAN KUMA; ‘Yan Sanda sun kame mutane 37 da laifuka a Jihar Katsina.