Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 20 ga Watan Satunba, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 20 ga Watan Satunba, 2019
1. Majalisar Wakilai sun Umarci CBN Da dakatar da Sabon Tsarin Kudi
Majalisar wakilan Najeriya ta karo na 9 ta umarci Babban Bankin Tarayyar Najeriya da dakatar da shirinta kan sabon manufar tsarin ajiyar kudade.
Ka tuna cewa Naija News ta ba da rahoton cewa CBN ta ba da umarnin aiwatar da wani sabon salo na manufofinta da zai kai ‘yan Najeriya da biyan wasu caji ga bankuna don ajiyar kudi a asusun kowace banki.
2. Shugaba Buhari zai Bar Najeriya Ranar Lahadi Don halartar Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya A Amurka
Ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Najeriya a karshen wannan makon zuwa Amurka, don halartar taro na 74 na Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA74).
Naija News ta samu labari da tabbacin tafiyar shugaban ne a bakin Tolu Ogunlesi, Mataimakin sa na musamman kan rariya, a wata sanarwa da ya bayar a layin yanar gizon nishadi ta Twitter.
3. Najeriya Ta Nemi sabon Rancen Kudi $2.5bn daga Bankin Duniya
Shugabancin Najeriya ta nemi Bankin Duniya don bada rancen dala biliyan 2.5, in ji Hafez Ghanem, mataimakin shugaban bankin duniya na Afirka.
A yayin da yake magana yayin wata hira da aka yi a ranar Laraba a Abuja, Ghanem ya bayyana da cewa har yanzu cibiyoyar kudin na duniya suna kan tattaunawa da gwamnatin Najeriya game da rancen.
4. Ekiti: PDP Ta Kalubalanci Fayemi Domin Nadin Alkalin Kotu da aka kora a Matsayin Shugaban SIEC
Jam’iyyar PDP ta reshen jihar Ekiti, ta kalubalanci Kayode Fayemi don nada Mai shari’a Jide Aladejana da aka sallama a baya a matsayin shugaban Hukumar Zabe ta Jihar Ekiti.
Jam’iyyar adawar ta yi ikirarin cewa nadin Jide a matsayin zai haifar da wasu nauyi a kan hukumar zaben.
5. Biafra: Nnamdi Kanu ya bayyana Abinda ya tattauna da UN
Shugaban kungiyar ‘Yan asalin yankin Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya bayyana da cewa ya gabatar da batutuwan da suka shafi mutanensa a gaban manyan kungiyoyi da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya (UN).
Naija News ta samu tabbacin bayanin Nnamdi Kanu ne a wata rahoton da ya fitar ta hannun sakataren watsa labarai da sakataren kungiyar IPOB, Emma Powerful, ya bayar a ranar Alhamis, 19 ga Satumba.
6. Osinbajo ya jagoranci Taron Majalisar Tattalin Arzikin Kasa
Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, A ranar Alhamis din da ta gabata ya jagoranci taron kwamitin tattalin arzikin kasar a fadar shugaban kasa, Abuja.
Naija News na da sanin cewa Mataimakin shugaban kasan, Osinbajo, bisa dokar da tsarin mulkin Najeriya, shine ke shugabancin Hukumar NEC.
7. Shugabannin Jam’iyyar PDP Sun Haɗu A Dubai Game Da Batun Karar Zaɓe
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya gana da mambobin kwamitin amintattu (BoT) na jam’iyyar game da hukuncin Kotun Shugaban kasa, ‘Petition Tribunal (PEPT)’.
Ka tuna da cewa Kotun sauraron karar shugaban kasa (PEPT) a ranar Laraba da ta gabata ta yi watsi da karar da PDP da dan takarar shugaban kasar, Alhaji Atiku Abubakar, suka gabatar.
8. Muna Aiki Fiye da Ministoci, Mun Dace kuwa da Motar SUVs mai Tsadar Biliyan N5.5bn – Majalisar Dattawa
Jagoran Majalisar Dattawa, Yahaya Abdullahi ya yi Allah wadai da koke-koke da al’ummar kasa ke yi game da matakin babban zauren majalisar ta na kashe Naira biliyan 5.5 a kan sayan motoci da ‘yan Majalisar.
A cikin bayanin Yahaya yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a ofishinsa da ke Abuja a ranar Laraba, Jagoran Majalisar Dattawan ya ce “cin mutunci ne ga jama’a da yin Allah wadai da matakin da ta yanke na kashe kudi kan siyan motoci”.
Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa