Uncategorized
Sabon Salo: Gwamna Nasir El-Rufai Ya Sanya Yaron sa a Makarantar Firamaren gwamnati

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir-El-Rufai ya jefa dan nasa, Abubakar Al-Siddique El-Rufai a makarantar firamare ta gwamnati a jihar.
Bisa rahoton da Naija News ta tattara, Gwamnan ya sanya Al-Siddique ne a dan Aji na Farko a Firamare ga makarantar Kaduna Capital School ranar Litinin.
Ka tuna a baya da cewa Jama’ar Jihar Kaduna, musanman kristocin jihar sun nuna rashin amincewa da komawar gwamnar El-Rufai a zaman jagoran Jihar a karo ta biyu.
Gwamnan ya bayyana a wata ganawa da yayi da manema labaran gidan Talabijin na ‘Channels Television’ a kwanakin baya kamin zaben Gwamnoni da cewa, “ko da na sanya Paparoma ne a matsayin abokin takara na ga kujerar Gwamna, Kiristocin Jihar da wadansu da suka rigaya suka kudura a zuciyansu, ba za su zabe ni ba.” inji Shi.