Connect with us

Labaran Najeriya

Jonathan yayi Bayani a kan Nadama game da Sadaukar da Shugabanci ga Buhari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yi wasu bayanan game da yanayin da ya shafi amincewarsa da ya yi karban kadara ga zaben shugaban kasa da aka yi a shekarar 2015 a Najeriya.

A cewar Jonathan, bai taba yin nadama ba a kan matakin da ya dauka ga daukar kadara da amincewa da nasarar shugaba Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa na shekarar 2015.

Ka tuna da cewa bayan da Hukumar gudanar da Hidimar Zaben Kasa (INEC) ta kamala zaben shugaban kasa ta shekarar 2015 da sanar da sakamakon, Goodluck Ebele Jonathan, Tsohon shugaban kasar ne na farko da buga kira ga shugaba Muhammadu Buhari don taya shi murna da nasara da zaben, bisa sakamakon da INEC ta gabatar.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa wannan matakin ya zan da mamaki ga wasu ‘yan Najeriya a yayin da ake zaton cewa Jonathan zai ki amincewa da sakamakon zaben da kuma ‘yin karar rahoton.

A wata sanarwa da aka bayar a kan labarai ‘yan kwanaki kadan da ta gabata,  Jonathan ya baiyana da cewa har gobe zai iya daukan irin wannan matakin sadaukarwar idan har hakan ne zai tabbatar da zaman lafiya a kasa.

KARANTA WANNAN KUMA; Jawabin Shugaba Muhammadu Buhari a Ranar ‘Yancin Kai ta Shekara 59 ga Najeriya.