Uncategorized
‘Yan Garkuwa sun Sace kimanin Mutane 9 a Abuja
Naija News ta karbi rahoton sabuwar harin mahara da bindiga a hanyar Abuja, ranar Litini da ta gabata.
Rahoton ya bayar da cewa kimanin mutane 9 ne mahara da bindigar suka sace a Pegi, wata karkara da ke a karamar hukumar Kuje, Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, a safiyar ranar Litini, 7 ga watan Aktoba da ta gabata.
Rahotannai sun sanar da cewa ‘yan harin sun yi shiga irin ta Sojojin Najeriya ne a yayin da suka fyauce da mutanen zuwa inda ba wanda ya san da shi.
Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Hukumar hana sha da Fataucin Miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta sanar da kama akalla mutane 21 da ake zargi da samar da magunguna ga ‘yan kungiyar Boko Haram a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba.
A ganewar Naija News Hausa, hade da dan karamin yaro mai shekara 12 ga haifuwa cikin mutane 9 da mahara da makamin suka sace a kan hanyar Abuja, koda shike har yanzu ba a gane da sunan yaron ba.