Connect with us

Uncategorized

Kogi: Ina da Shaidar Da Ya Nuna Cewa Gov Yahaya Bello Zaiyi Makirci A Zaben Asabar – Dino

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Dan jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP da kuma dan takarar kujerar Sanata a ‘Kogi West Senatorial’ a zaben na ranar Asabar, Dino Melaye, ya yi ikirarin cewa an riga an sanya tsare-tsare domin kadamar da makirci a zaben da za a gudanar a gobe, Asabar, 16 ga watan Nuwamba.

Dino ya jadada da cewa lallai akwai shirin don sayar da zaben gobe ga gwamnan jihar, Yahaya Bello da kuma Smart Adeyemi, dan takaran gidan Majalisa.

Sanata Dino Melaye a cikin zarginsa ya bayyana da cewa yana da shaidar shirin makircin ne a cikin wata bidiyo da ya nuno lokacin da Gwamna Bello da ‘yan ta’addansa ke ganawarsu don kadamar da makircin a yayi zaben ranar Asabar.

A yayin bayyana tabbacin shaidar, Dino Melaye a cikin jerin sakonansa da ya aika a shafin Twitter, ya kuma bayyana wasu daga cikin ajanda da aka cimma a wurin taron wanda ya hada da kwace akwatunan zabe da sauransu dai.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Babban Jam’iyyar Adawar kasa, PDP ta zargi Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, da darakta-janar na kamfen din sa da shirin kamu da tsare Sanata Dino Melaye gabanin zaben ranar 16 ga Nuwamba.

Jam’iyyar adawar ta lura da cewa an gabatar da shirin ne a ranar Litinin, 4 ga watan Nuwanba da ta wuce yayin wani taro da aka yi a gidan Gwamnatin Jihar.

Ka tuna da cewa a cikin wata bidito da Naija News Hausa ta rabar, an gano gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai yana durkusawa da gwiwowinsa da rokon jama’ar jihar Kogi da su yafe wa Bello, su zabe shi a karo na biyu a matsayin Gwamna.

Naija News ta fahimci cewa wannan ya faru ne a ranar Alhamis 14 ga Nuwamba da ta wuce, lokacin da Jam’iyyar ‘All Progressives Congress’ (APC) ke hidimar ralin neman zabensu a Lokoja, babban Jihar Kogi.