Connect with us

Labaran Najeriya

PDP: Atiku Ya Cika Shekara 73 Ga Haifuwa – Ga Sakon Peter Obi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mataimakin Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party, Peter Obi, a ranar Litinin, ya taya tsohon Mataimakin Shugaban kasar Najeriya da kuma dan takaran shugaban kasa a zaben 2019 a jam’iyyar, Atiku Abubakar, da murnar cikar sa shekara ta 73 da haihuwa.

Tsohon gwamnan jihar Anambra din, Obi ya bayyana dan takarar shugaban kasar na PDP a matsayin babban jagora da kuma aboki.

Perter Obi a yayin taya Atiku murna da karin shekarun ya wallafa sakon gaisuwa da tayin murna a shafin nishadantarwa ta Twitter, ya ce;

“Ina murnar zagayowar ranar haihuwar babban shugaba da aboki, @atiku”

“Madauwami kake ta hanyar sadaukarwa da kishin kasa. Yayin da tsufa, haka kuwa ƙarfinka zai karu. Tare da fatan alheri daga gare ni.”

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya aika sakon Murna da karin shekaru ga Goodluck Jonathan, tsohon shugaban kasar Najeriya.

A cikin sakon shugaban, ya yaba wa Goodluck da ya yi imanin cewa halin kaskantar da kai da kishin kasa da tsohon Shugaban kasar ke da shi zai ci gaba da yaduwa a fadin kasar, tare da fadakar da al’ummomi da za su zo kan sadaukarwar musanman don dorewar dimokiradiyya da kuma samar da ci gaba mai dadewa a kasar.