Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 25 ga Watan Nuwamba, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 25 ga Watan Nuwamba, 2019
1. Manya Ga APC Na Yunkurin Neman Shugaba Buhari Da Sake Shugabanci A Shekara Ta 2023
Wani jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta reshen jihar Ebonyi, Charles Enya, ya shigar da kara wanda ke neman a yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima domin bai wa Shugaba Muhammadu Buhari damar tsayawa takara a karo na uku.
Enya, wanda ya kasance sakataren shirye shirye ga shugaba Buhari yayin babban zaben shekarar 2019, ya shigar da karar mai lamba (FHC/AI/CS/90/19) a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abakiliki, bisa rahoton da aka bayar a hannun jaridar Daily Trust.
2. Kogi: Tsohon Dan Majalisar Dokoki Yayi Murabus da PDP, Wata kila Zai koma ga APC
Wani tsohon dan majalisar tarayya da ya wakilci mazabar tarayya ta Yagba a majalisar wakilai, Hon. Karimi Sunday Steve ya fice daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Tsohon dan majalisar wanda har yanzu bai bayyana sabuwar jam’iyyarsa ba, ana rade-radin cewa yana tunanin shiga Jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
3. Shugaba Buhari Ya Mayar da Martani Ga Kisan Shugaban Mata na PDP da aka Yi
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da abin da ya bayyana a matsayin “kisan gilla” na shugaban matan ‘yan jam’iyyar PDP na jihar Kogi, Malama Achejuh Abuh.
A cikin sanarwar fadar Shugaban kasa ta ranar Lahadi da aka bayar ta hannun mai taimakawa shugaban kasar kan harkokin yada labarai, Mista Femi Adesina, Buhari ya yi kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar da kamo wadanda suka kashe matar.
4. Matsawa: Sanatoci Sun cire hukuncin kisa ga kalaman kiyayya
Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya ce za a cire sammacin hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da kalaman batanci da kalaman Kiyaya da ya gabatar ga majalisar dattawa.
A cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, Mataimakin Whip na Majalisar Dattawar ya ce zasu yi gyara akan kudurin na kalaman kiyayya don tabbatar da cewa ka’idojin da ke kunshe cikin kudurin dokar za su yi daidai da ra’ayin ‘yan Najeriya.
5. Kogi: Dino Melaye Zai Sake Fadi Zabe – APC Ta gayawa PDP
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Lahadi ta ce Sanata Dino Melaye da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun riga sun fadi zaben Kogi West da ake shirin yi nan mako ta gaba.
Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa, Hukumar gudanar da hidimar Zaben kasar (INEC) ta sanya ranar Asabar, 30 ga Nuwamba, don gudanar da zaben sake maye gurbin Yammacin Kogi.
6. Biafra: Nnamdi Kanu ya Bayyana Wadanda Suka Fara Zancen Kiyayya a Najeriya
Jagoran kungiyar ‘Yan asalin yankin Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya zargi marigayi Sarduana na Sakkwato, Sir Ahmadu Bello, da asalin haifar da kalaman kiyayya a Najeriya.
Ku tuna cewa a kokarin magance da dkile wasu masu amfani da kafafen yada labarai a kasar don yada kalaman batanci da kuma kiyayya, tsohon kakakin majalisar dattijai, Sabi Abdullahi ya sake gabatar da Dokar ‘Kalaman Batanci” a majalisa.
7. Aisha tayi Adawa da Yunkurin Neman Wa’adin mulkin na Karo Uku ga Shugaba Buhari
Wakilin kungiyar ‘Bring Back Our Girls’ (BBOG), Aisha Yesufu, ta yi adawa da wa’adi na uku na Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin Shugaban Najeriya.
Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa Malama Yesufu ta harzuka wa’adin shugaban na uku a kan karagar mulki cikin wata faifan bidiyo mai mintina biyu da sakan ashirin da ta jefa a shafin yanar gizo, watau Twitter, ranar Lahadi da yamma, 24 ga Nuwamba.
8. Bayelsa/Kogi: Buhari da APC hade da INEC Suna Nakasa Dimokradiyya – PDP
Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), na zargin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da All Progressives Congress (APC) da kokarin lalata da nakasar da dimokiradiyya a Najeriya.
A wata sanarwa ranar Lahadi dauke da sa hannun sakataren watsa labarai na kungiyar, Kola Ologbondiyan, PDP ta ce Shugaban Hukumar Zaben kasar (INEC), Mahmood Yakubu shi ne “mafi munin jagoran hukumar INEC” a tarihin siyasar Najeriya.
Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa