Connect with us

Uncategorized

PDP: Yakubu Dogara ya bayyana dalilin da ya sa ya bar Jam’iyyar APC zuwa PDP

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kakakin yada yawun Gidan Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya gabatar da dalilin da ya sa ya janye daga Jam’iyyar APC zuwa Jam’iyyar PDP.

Mun sanar a Naija News Hausa a ranar Talata da ta gabata da cewa Kakakin yada yawun Gidan Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara yayi murabus da Jam’iyyar APC ya kuwa koma wa tsohon Jam’iyyar sa PDP.

Muna da sani a Naija News da cewa Yakubu Dogara da ma dan Jam’iyyar PDP ne, kuma daga Jam’iyyar aka zabe shi zuwa zaman gidan Majalisar Wakilai.

Dogara ya janye ne daga Jam’iyyar APC tare da wasu ‘yan Majalisa biyu Edward Pwajok daga Jihar Plateau da Ahmed Yerima daga Jihar Bauchi.

Dogara ya bayyana da cewa ya shiga Jam’iyyar APC a wata Mayu a shekara ta 2017 a lokacin da ya kula da matsaloli a Jam’iyyar PDP.

Ya ce “Na janye ne daman daga Jam’iyyar PDP lokacin da wata matsala ta taso a Jam’iyyar da har ya raunana ni da gaske”.

“Da baya ne Kotun kara ta gabatar da cewa babu wata tsatsaga a Jam’iyyar PDP” in ji Dogara.

“Tun lokacin kuwa Jam’iyyar PDP ta sake tsari kuma ba wata makirci a cikin ta tun daga wannan lokacin har yanzu”.

“Ina sanar maku a yau da cewa na komawa Jam’iyyar da dama nike, Jam’iyyar da ta kaini gidan Majalisa, Jam’iyyar da kuma ke da kyakyawar shiri don mayar da kasar Najeriya yada ya kamata” in ji shi.

Karanta kuma: Gwamnan Jihar Borno, Shettima ya sanya Mafarauta ga yaki da Boko Haram