Connect with us

Labaran Najeriya

PDP/APC: Buhari shigar da ‘yan ta’addan kasar Nijar zuwa Jihar Kano – Atiku

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar  ya zargi shugaba Muhammadu Buhari da kwaso ‘yan ta’addan kasar Nijar zuwa wajen hidimar neman zaben sa a Jihar Kano.

Muna da sani a Naija News da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya shiga Jihar Kano a ranar jiya don kamadar da hidimar yakin neman zaben sa a Jihar, muna kuma samu rahoto da cewa baki daga kasar Nijar sun halarci hidimar yakin neman zabe na shugaba Buhari da aka yi a Jihar Kano.

Atiku ya aika a shafin nishadarwan twitter na Jam’iyyar da zargin cewa shugaba Muhammadu Buhari ya shigo ne da ‘yan ta’adda daga kasar waje.

“Menene suka zo yi, menene mahadin su da yakin neman zaben, menene ta su a cikin zaben Najeriya?, wannan shi ne tambayar Atiku ga shugaba Buhari”

sakon na kamar haka a turance:

“Da irin wannan ziyarar, mun bukaci bayyanin abin da ‘yan siyasar Nijar da ‘yan ta’addan su suka zo yi a wajen hidimar Jam’iyyar APC” inji Atiku.

Mun sanar da safen nan a Naija News da cewa wasu ‘yan Najeriya sun aika a shafin twitter da cewa #BabaYaKasa, ba su bukatar Buhari a mulki kuma.