Labaran Najeriya
Oby Ezekwesili tayi murabus da tseren takaran Shugaban Kasa daga Jam’iyya ACPN
‘Yan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar ACPN, Oby Ezekwesili ta yi murabus da Jam’iyyar bayan janyewar ta a tseren takara a makonnai da ta wuce.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Oby ta sanar da cewa ta janye daga tseren takaran shugaban kasa daga Jam’iyyar ACPN.
Mun samu rahoto a yau da cewa Oby ta mayar ma Jam’iyyar ACPN da katin mamba nata, da kuma duk wasu kayaykin da ta kumshi Jam’iyyar da ke a hannun ta.
‘Yar takaran ta gabatar da barin Jam’iyyar ne a yau a wata zaman tattaunawa da Manema labaran Duniya da ta gudanar .
“Na bar Jam’iyyar ACPN ne don na gane da cewa Jam’iyyar bawai sun damu ne da ci gaban kasa ba, sai dai son kudi kawai ba wata guri” inji Oby Ezekwesili.
Ko da shike a baya da Ezekwesili ta gabatar da matakin ta na janye wa tseren, wasu mambobin Jam’iyyar sun bayyana bacin ran su da wannan.
Duk da hakan Oby ba ta canza da ra’ayin ta ba.
Ta ce “Jam’iyyar ba ta da wata guri da ko ganin gaba da kasar Najeriya, iya son kudi kawai”
Karanta wannan kuma: An bada naira Miliyan 45 ga yankuna don ‘sayen hankalin mutane ga fitar ralin Buhari -inji Kakakin yada yawun hidimar zabe na Jam’iyyar PDP, Mallam Buba Galadima.