Uncategorized
APC: ‘Yan Hari da bindiga sun kashe wani ciyaman na Jam’iyyar APC a Jihar Imo
Wasu Mahara da bindiga da ba a gane da su ba, sun kashe Ifeanyi Ozoemena, ciyaman na Jam’iyyar APC ta yankin Logara/Umuohiagu, a karamar hukumar Ngor Okpala ta Jihar Imo.
Rahoto ta bayar da cewa an kashe Ifeanyi ne dadaren ranar Talata da ta wuce bayan wata ganawa da yayi da ‘yan jam’iyyar da ke yankin.
Wannan mugun abin ya jawo tsoro kwarai da gaske a zuciyar mutanen yankunan musanman akan zaben shugaban kasa da na gidan majalisar dattijai da za a gudanar a ranar Asabar ta makon nan.
Abin tausayi da takaici, a bayar da cewa ‘yan harin sun kashe Ifeanyi ne a gaban iyalan sa. “A halin yanzun mutanen yankin na cikin wata halin tausayi da tsoro” inji Mai unguwan yankin, Sarki Martin Opara.
“Ba mu taba karo da irin wannan cin mutunci da kashe rai ba ga zabe sai a wannan karo” inji Opara.
“Na kalubalanci hukumomin tsaron kasa da ganin cewa sun kame wadanda suka aikata irin wannan mumunar abin cikin gaggawa ba tare da jinkiri ba,” inji shi.
“An san da kauyan Logara da zamantakewa ta kwarai da lafiya, amma wannan karon abin ya canza” inji.
Kwamishanan ‘Yan Sandan Jihar, Mista Dasuki Galadanchi ya fada akan layi da cewa ‘yan sanda sun rigaya sun dauki gawar sa kuma an adana shi.
Har yanzun dai ana kan bincike da neman wadanda su ka aiwatar da irin wannan abin.
Mun ruwaito a baya da cewa ‘Yan Hari da makami sun kashe Boniface, Ciyaman na Jam’iyyar APC na Jihar Benue
Duk da cewa jami’an ‘yan sanda sun yi baraza a baya da cewa zasu samar da isashen tsaro a kasa, musanman lokacin zaben 2019.