Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 26 ga Watan Fabrairun, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 26 ga Watan Fabrairun, 2019
1. Hukumar INEC ta fara sanar da sakamakon kuri’u zaben shugaban kasa
Hukumar gudanar da zaben kasar Najeriya (INEC) ta fara gabatar da rahoton kuri’un zaben shugaban kasa da ta gidan Majalisai na zaben da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata a jihohin kasar.
Hukumar ta fara sanar da sakamakon ne a jagorancin Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu.
2. Anyi makirci da yawa ga zaben 2019 don taimakawa Buhari – inji Nnamdi Kanu
Shugaban Kungiyar Iyamirai ta Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya bayyana da cewa anyi makirci da yawa ga zaben shugaban kasa ta wannan shekarar don taimakawa shugaba Muhammadu Buhari ga lashe zaben.
Nnamdi Kanu ya gabatar da hakan ne kamar yadda ya aika a shafin yanar gizon nishadarwan sa ta twitter a ranar Litinin, 25 ga watan Fabrairu, 2019 da cewa an gudanar da makirci kwarai da gaske ga zaben don tallafa wa Buhari da cin nasara.
3. Shekarau ya lashe zaben kujerar Sanata a Jihar Kano
Hukumar INEC ta gabatar da dan takaran kujerar Sanata na Jihar Kano daga Jam’iyyar APC, Malam Ibrahim Shekarau a matsayin mai nasara ga lashe zaben kujerar dan Majalisa a Jihar.
Muna da sani a Naija News Hausa da cewa tsohon gwamnan Kano, Shekarau ya fita tseren takaran dan Majalisan Dattijai ne a karkashin Jam’iyyar APC.
4. Jam’iyyar PDP ta bayyana rashin amincewa da rahoton da hukumar INEC ke gabatarwa
Jam’iyyar dan takaran shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, PDP sun gabatar da rashin amincewar su da rahoton da Hukumar gudanar da zaben kasa, INEC ke ta bayarwa.
Jam’iyyar sun gabatar da wannan ne a ranar Litinin da ta gabata daga bakin Uche Secondus, Ciyaman na Jam’iyyar PDP ta tarayya, da cewa rahoton kuri’u da hukumar INEC ke gabatarwa ba gaskiya bace.
5. Rundunar Sojojin Sama sun ci nasara da wasu ‘yan ta’adda a Jihar Borno
Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya, Air Task Force (ATF) a rukunin Operation Lafiya Dole sun bayyana wata nasara da suka yi da rukunin ‘yan ta’addan Islam da aka fi sani da suna (ISWAP) ta yankin Kolloram a Jihar Borno.
Sun samu tabbacin hakan ne a Naija News ranar Litinin da ta gabata, daga bakin, Kamrad Ibikunle Daramola, Mai yada labarai ga rundunar Sojojin Sama ta Najeriya.
6. Atiku ya fadi ga zaben kananan hukumomin Jihar Kano duka
Dan takaran shugaban kasa daga Jam’iyyar APC, shugaba Muhammadu Buhari ya lashe zaben kananan hukumomi 34 da ke a jihar Kano.
A halin yanzu, Naija News Hausa ta gane da cewa shugaba Muhammadu Buhari na jagoran dan takaran shugaban kasa na Jam”iyyar PDP, Atiku Abubakar da kuri’u kimanin 800,000.
7. 23 ga Watan Fabrairu, ranar ce na kubuta ga Jihar Kwara – inji Lai Mohammed
Ministan Yada Labarai da Al’adun kasa, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana a karkashin Jam’iyyar APC da cewa Jihar Kwara za ta ci gaba da murna da tunawa da ranar 23 ga watan Fabrairu na kowace shekara a matsayin ranar kubuta daga tsananci da wahala.
”Ina bukatar Gwamnan Jihar Kwara, a bayan an rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayu, shekara ta 2019, ya gabatar da ranar 23 ga Watan Fabrairu na kowace shekara a matsayin ranar kubuta ga Jihar” inji Mohammed.
8. Shugaba Buhari ya yi bayani game da sakamakon zabe
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a komawarsa birnin Abuja bayan jefa kuri’ar sa na zaben shugaban kasa da ta Majalisai a kauyan Daura ranar Asabar da ta gabata ya yi furci game da rahoton zabe.
Buhari ya fada da cewa zai jira har hukumar gudanar da zaben kasar, INEC ta sanar da sakamakon zaben maimakon jita-jita daga ko ta ina akan rahoton zaben.
Ka samu cikakken labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa