Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumm’a, 1 ga Watan Maris, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 1 ga Watan Maris, 2019

1. Atiku bai kadarci shugabancin kasar Najeriya ba  – Inji Oshiomhole

Babban Ciyaman na Jam’iyyar APC ta tarayya, Adams Oshiomhole, ya bayyana a wata gabatarwan sa da cewa Atiku Abubakar, dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar adawa, PDP bai kadarci shugabancin kasar ba.

“Atiku na da tsananci ne kawai, bai da kadaran shugabancin kasar Najeriya” inji shi.

Wannan itace fadin Adams Oshiomhole a ranar Alhamis da ta gabata a wata zaman tattaunawa da Jam’iyyar APC sunka gudanar a birnin Abuja.

2. Shugabancin kasa ta kafa aiki akan kanancin kudin ma’aikata na 30,000

Boss Gida Mustapha, babban sakataran gwamnatin tarayya ya bayyana da cewa gwamnatin tarayya ta samar da yadda za a kadamar da biyar kanancin albashin ma’ikatan kasa na naira dubu 30,000 da aka amince da ita kwanakin baya.

Mustapha ya gabatar da wannan ne a ranar Alhamis da ta gabata a birnin tarayya, Abuja a lokacin da yake bayani da manema labarai.

3. Kotun Jihar Rivers ta soke wani dan takaran gwamnan Jihar

Babban Kotun kara ta birnin Port Harcourt, a Jihar Rivers da sanar da dakatar da Dumo Lulu-Briggs daga tseren takaran kujerar gwamna daga Jam’iyyar ‘Accord Party’ a Jihar.

Alkalin da ke karar, Justice E.A Obile ya bayyana da cewa Dumo Lulu-Briggs bai fita ga zaben firamare ba, saboda haka bai dace ba ya fita tseren takaran gwamnan Jihar ba.

4. Mun dakatar da Alkali Onnoghen ne kawai, bamu tsige shi ba  – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya da Babban alkalin hukuncin kasa sun bayyana ga kotun kara a ranar Alhamis da ta gabata da cewa ba wai sun tsige babban Alkalin kotun Najeriya, Walter Onnoghen ba ne, da cewa sun dakatar da shi ne kawai.

Mun sanar a Naija News Hausa a can baya da cewa an dakatar da babban alkalin kotun Najeriya, Walter Onnoghen.

5. Rasaq Atunwa ya karyace zance cewa ya janye daga tseren takaran Gwamna

Dan takaran Gwamnan Jihar Kwara daga Jam’iyyar PDP, Razak Atunwa, ya yi watsi da jita-jitan cewa ya janye daga tseren takaran kujerar gwamnan Jihar Kwara.

Muna da sani a Naija News da cewa hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) sun gabatar da ranar 9 ga watan Maris a matsayin ranar da za ta gudanar da zaben Gwamnonin Jihar kasar Najeriya.

6. ‘Yan hari da bindiga sun kai sabuwar hari a Jihar Zamfara

Mahara da bindiga sun sake kai wata sabuwar farmaki a wata kauyan Jihar Zamfara da ake kira Anka.

An bayyana kamar yadda muka samu rahoto da cewa ‘yan harin sun fada wa mutanen Kawaya ne da ke a kauyan Anka ta Jihar Zamfara, inda suka lallace gidajen mutane, da motoci, harma da baburan su.

Abin takaici, mutane goma sha ukku suka rasa rayukansu sakamakon harin.

7. Ba mu damu da karar da Atiku ke batun yi ba – inji Shugabancin kasa

Babban sakataren gwamnatin tarayyar kasa, Boss Mustapha (SGF) ya ce “babu abin damuwa game da barazanar Atiku ke yi na kara akan zaben shugaban kasa ta ranar Asabar da ta gabata”.

Mu iya ganewa a Naija News Hausa da cewa dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana da cewa bai amince da sakamakon zaben 2019 da hukumar INEC ta gabatar da ita ba.

8. Mai yiwuwa shugaba Buhari ya sake tsarafa shugabancin sa

Kakakin yada yawun shugaban kasa, Femi Falana, ya gabatar da cewa mai yiwuwa shugaba Muhammadu Buhari ya sake tsarafa rukuni da ke cikin shugabancin sa kamin ranar 29 ga watan Mayu.

Mun tuna a baya da cewa ya dauki shugaban tsawon watannai shidda a shekarar 2015 da ya hau kujerar mulki kamin ya gabatar da rukunin da zasu yi aikin shugabancin tare da shi.

9. Tsohon shugaban Sojojin sama, Tony Omenyi zai yi jarun shekara bakwai

Babban Kotun Koli ta birnin Abuja a yau ta gabatar da jarun tsawon shekaru bakwai (7) ga wani tsohon shugaba  a rundunar sojojin sama ta Najeriya, AVM Tony Omenyi.

Naija News ta gane da cewa bada wannan hukuncin ne ga Mista Omenyi akan wata zargi cin hanci da rashawa da aka gane da shi na kimanin kudi naira miliyan N136 da ya karba daga hannun wata kamfanin aiki.

10. Tsohon shugaban kasar Najeriya ya gudu daga Najeriya a wata Bidiyo

Wata bidiyo ta mamaye yanar gizo. Bidiyon na dauke da tsohon shugaban kasa Najeriya, Olusegun Obasanjo, inda aka nuno shi yana a gaggauce a cikin filin jirgin sama don barin kasar.

Ko da shike a baya Obasanjo a wata sanarwa ya yi watsi da jita-jitan cewa ya bar kasar Najeriya.

 

Ka samu cikakken labaran kasar Najeriya a shafin Naija News Hausa