Uncategorized
An kame wani da Takardun zabe a Jihar Kaduna
Jami’a tsaron ‘Yan Sandan Jihar Kaduna sun kame wani da takardun zabe
A yayin da ake cikin gudanar da hidimar zaben Gwamnoni da ta Gidan Majalisar Wakilan Jiha a Jihar Kaduna, ‘Yan Sanda sun gano wani da ake zargi da yiwa Jam’iyyar APC aiki a Jihar da takardun zabe.
Naija News Hausa ta gane da hakan ne a yayin da ‘yan sandan jihar suka kame wani mai suna Samuel Semion a runfar zabe na Manchok (RAC), ta karamar hukumar Kaura.
Jami’an tsaron sun kame Mista Semion ne da takardun zabe a Uguwan Aba Dube I, watau a runfar zabe da ke a yankin Manchok RAC. Bayan da aka kame shi, ya bayyana da ‘yan sanda da cewa wani babban mamban jam’iyar su ne ya rabar da takardan ga masu wakilcin jam’iyyar a kowace runfar zabe da ke Jihar.
An samu nasarar kame shi ne bayan da Malaman hukumar INEC da ke a yankin a jagorancin Mista Cletus Joseph, watau shugaban gudanar da hidimar zaben yankin ya gane da harkan. Ya kuma sanar ga jami’an tsaro a gaggauce da cewa su kame Simon.
“Ina mai fadi gaba gadi da cewa ba wani wakilin jam’iyya da ke da daman rike kayan zabe, musanman takarda ko rajista na zabe” Malamin zaben.
Rahoto ta bayar da cewa Ofisan hukumar ‘yan sanda da ke yankin, CSP Daniel Mbwale, ya bada umarni ga darukan tsaro da kwace takardan daga hannun dukan wakilan jam’iyyo da ke a yankin.