Uncategorized
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litinin, 11 ga Watan Maris, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litinin, 11 ga Watan Maris, 2019
1. Mutane 157 sun rasa rayukan su ga hadarin Jirgin sama da ya fashe a Ethiopia
Wata jirgin Sama a kasar Ethiopia ta fashe a shiyar Addis Ababa-Nairobi a safiyar ranar Lahadi da ta gabata.
Naija News ta gane da cewa mutane 157 da ke cikin jirgin sun mutu duka, kamar yadda rahotannai suka bayar.
“Mun gabatar da hadarin jirgin saman mu mai lamba ET 302 a dake kan tafiya daga yankin Addis Ababa zuwa Nairobi” inji kamfanin jirgin saman a lokacin da jirgin ya fashe.
2. Hukumar INEC ta dakatar da zaben Jihar Rivers zar zuwa gaba
Hukumar gudanar da hidimar zaben kasa (INEC), sun gabatar da dakatar da zaben Jihar Rivers zar zuwa gaba akan wasu sharidun zabe da aka karya.
Hukumar sun gabatar da wannan sanarwan ne a ranar Lahadi da ta gabata daga bakin Mista Festus Okoye, Ciyaman na hukumar INEC ta fannin yada labarai.
3. PDP: Hukumar INEC ta gabatar da Okezie Ikpeazu mai nasara ga kujerar Gwamnan Jihar Abia
Hukumar ta gabatar da Okezie Ikpeazu, Gwamnan da ke kan mulkin Jihar da kuma dan takaran kujerar gwamna na karo biyu daga Jam’iyyar PDP a matsayin mai nasara ga zaben.
Farfesa Damian Ozurumba, Malamin zaben da ke jagorancin zaben yankin ya gabatar da cewa dan takaran ya lashe kujerar ne da kuri’u 261,127 fiye da dan adawan sa a Jihar.
4. Abdulrahman Abdulrazaq ya lashe kujerar Gwamnan Jihar Kwara
Dan takaran kujerar gwamna daga daga jam’iyyar APC, Mista Abdulrahman Abdulrazaq, ya lashe zaben kujerar gwamna a Jihar Kwara da aka yi a ranar Asabar da ta gabata.
Abdulrahman ya lashe tseren ne da kuri’u 331,546 fiye da dan adawan sa daga jam’iyyar PDP, Mista Abdulrazaq Atunwa, da ke da kuri’u 114,754.
5. Jami’an ‘Yan Sanda sun gano jigon Jam’iyyar PDP, Emilia Nte da aka sace
Jami’an tsaron ‘yan sandan Jihar Rivers sun samu ribato wata jigo a jam’iyyar PDP, Emilia Nte da ‘yan ta’adda suka tafi da ita a wata ganawar wuta a ranar 8 ga watan Maris da ya gabata.
Naija News Hausa na da tabbacin ribato tsohon ciyaman na karamar hukumar Andoni, Emilia Nte da ‘yan hari da bindiga suka sace a kwanakin baya a gidan ta da ke Uyeada, a Jihar Rivers.
6. APC: Sanwo-Olu ya lashe kujerar Gwamnan Jihar Legas
Hukumar INEC ta gabatar da dan takaran kujerar Gwamna daga jam’iyyar APC, Mista Babajide Sanwo-Olu, a matsayin mai nasara ga zaben kujerar gwamna na Jihar Legas sakamakon yawar kuri’u ga zaben ranar Asabar da aka gudanar a Jihar.
Dan takaran ya lashe kujerar ne da kuri’u 533,304 fiye da dan adawan sa daga jam’iyyar PDP, Jimi Agbaje, mai kuri’u 206,141.
7. Rundunar tsaron kasa sun kashe ‘yan Boko Haram 50, sun kuma kame mutum daya
Hadaddiyar Rundunar Tsaron Kasa ta (MNJTF) sun rutsa da ‘yan ta’adda Boko Haram, sun kuma ci nasara da harin wajen kashe mutum 50 da kuma kame mutum guda da rai.
Jami’an tsaron sun gabatar ne ga manema labarai a birnin Abuja da cewa sun kashe ‘yan ta’addan ne tsakanin ranar Jumma’a da Asabar da ta gabata a yankunoni daban daban. Kamar yadda Col. Timothy Antigha, Ofisan yada labarai ga hukumomin tsaron.
8. Abubakar Sani Bello ya lashe kujerar Gwamnan Jihar Neja a karo ta biyu
Gwamnan da ke a kan mulki a Jihar Neja, Gwamna Abubakar Sani Bello ya sake lashe kujerar mulkin Jihar a karo ta biyu, daga jam’iyyar APC.
Naija News Hausa ta gane da cewa Gwamna Bellow ya lashe kujerar ta cin nasara ga kananan hukumomin 24 daga cikin hukumomi 25 da ke a Jihar.
9. Shahararren dan wasan fim na Nollywood, Desmond Elliot ya ci kujerar dan majalisar Jihar Legas
Hukumar gudanar da zaben kasa (INEC), ta gabatar da shahararren dan shirin wasan fim na Nollywood ta Najeriya, Desmond Elliot da ke takaran kujerar gidan majalisar wakilai a Jihar Legas daga jam’iyyar APC a matsayin mai nasara ga tseren takaran.
Malamin zabe da ke jagoran zaben yankin, Dakta Bolajoko Dixon-Ogbechi ya gabatar da hakan ne a ranar Lahadi da ta gabata a karamar hukumar Surulere, a Jihar Legas.
Ka samu cikakkun labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa