Uncategorized
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 27 ga Watan Maris, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 27 ga Watan Maris, 2019
1. Ifeanyi Ubah ya karyace zancen komawa Jam’iyyar APC
Sanatan da ke wakilcin Jihar Anambra ta Kudu, Sanata Ifeanyi Ubah daga Jam’iyyar YPP ya bayyana da cewa ba wai ya koma ga jam’iyyar APC ba ne kamar yada ake fadi.
“Na halarci zaman Jam’iyyar APC ne kawai don yin hurda da jam’iyyar da ke kan shugabancin kasa” inji Ifeanyi Ubah
2. Marafa yayi bayani akan Jam’iyyar APC ta Jihar Zamfara
Sanata Kabiru Marafa ya jinjina wa Kotun Kara ga matakin da ta dauka da dakatar da ‘yan takaran Jam’iyyar APC daga zaben Jihar ta shekarar 2019.
Naija News Hausa na da sanin cewa Kotun Kara ta Jihar Sokoto a ranar Litinin da ta wuce ta gabatar da janye karar zaben Firamare ta Jihar Zamfara jagorancin Alkali Tom Yakubu.
3. Kotu ta bayar da dama ga Hukumar INEC don kamala zaben Jihar Adamawa
A ranar Talata, 26 ga watan Maris 2019 da ta gabata, Alkali Abdulaziz Waziri daga Kotun Koli ta Jihar Yola, babban birnin Jihar Adamawa, ya gabatar da bada dama ga Hukumar INEC don ci gaba da kadamar da hidimar zaben Jihar.
Kotu ta dakatar da hukumar INEC ga gudanar da zaben Jihar ne akan wata karar da dan takaran kujerar gwamnan Jihar daga Jam’iyyar (MRDD), Mustafa Shaba, ya gabatar ga kotun kwanakin baya da suka shige.
4. Karya ne, ban bada naira Miliyan N200m ga Akpo Bomba ba – inji Wike
Gwamna Jihar Rivers, Nyesom Wike yayi watsi da zancen cewa ya bayar da kudi kimanin naira Miliyan N200m ga Akpo Bomba Yeeh, mataimakin dan takaran kujerar Gwamnan Jihar daga Jam’iyyar AAC don komawa ga Jam’iyyar PDP.
Naija News Hausa ta tuna a baya da cewa Akpo Bomba Yeah ya gabatar ga fili da janyewar sa daga jam’iyyar AAC da kuma komawa ga Jam’iyyar PDP.
5. Hukumar INEC ta bayyana lokacin da zata bawa Adeleke takardan komawa kan mulki
Hukumar gudanar da hidimar zaben kasa, INEC ta gabatar da lokacin da za ta bayar da takardan komawa ga kujerar mulki ga Sanata Ademola Adeleke, Sanatan Jam’iyyar PDP daga Jihar Osun.
Naija News Hausa ta tuna a baya da cewa Kotun Kara ta dakatar da Gboyega Oyetola daga shugabancin Jihar, ta kuma gabatar da Adeleke a matsayin Gwamnan Jihar.
6. Hukumar INEC ta gabatar da ranar da za ta kadamar da zaben Jihar Adamawa
Hukumar kadamar da zaben kasar Najeriya, INEC ta gabatar da ranar 28 ga watan Maris 2019, watau Alhamis ta gaba don kadamar da zaben kujerar gwamna na Jihar Adamawa ga zaben 2019.
Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa Kotu ta janye karar da ake akan zaben Jihar Adamawa.
7. Ku janye bakin ku da zargin Sanata Saraki akan shugabancin gidan Majalisa, PDP ta gayawa APC
Rukunin Jam’iyyar PDP ta gidan Majalisar Dattijai sun kalubalanci ‘yan Jam’iyyar APC ta gidan Majalisar da janye jita-jita da suke yi akan shugaban gidan Majalisar, Sanata Bukola Saraki.
Jam’iyyar PDP sun fadi hakan ne don mayar da martani akan jita-jita da jam’iyyar APC ke yi na cewar Bukola Saraki na kokarin ya ci gaba da cin albarkacin shugabancin gidan majalisar bayan ya sauka kan kujerar.
8. Hukumar INEC ta dakatar da bayar da takardan mulki a Jihar Zamfara
Hukumar gudanar da zaben kasar Najeriya (INEC) ta dauki mataki kan shari’ar da Kotun Kara tayi na dakatar da jam’iyyar APC ta Jihar Zamfara ga samun daman shiga tseren zaben kujerar Gwamna a Jihar, kamar yadda aka gabatar a ranar Litini da ta gabata.
Naija News ta gane da hakan ne a yayin da Alkali Tom Yakubu daga Kotun kara ta Jihar Sokoto ya gabatar da karar a ranar Litini da ta gabata.
Ka samu karin labaran kasar Najeriya a shafin Naija News Hausa