Connect with us

Uncategorized

Daktoci daga kasar Turai sun shigo Najeriya don binciken lafiyar jikin Sheik El-Zakzaky

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wasu daktoci a jagorancin Hukumar IHRC, daga kasar Turai sun shigo Najeriya don diba lafiyar jikin shugaban kungiyar cigaban Addinin Musulunci ta kasar Najeriya (IMN) da aka fi sani da suna ‘Yan Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, da Matarsa Zinat.

Ka tuna da cewa Gwamnatin Tarayyar kasar Najeriya a shekarar 2015 da ta gabata, sun kame El-Zakzaky da Matan shi da zargin kisa da wasu zargi kuma dama da aka gabatar a kansu.

Bisa rahoto, Naija News ta gane da cewa an shigo ne da Daktocin don diban lafiyar jikin Sheikh ne da Matar sa. Wannan kuma zai dauki tsawon kwanaki kadan, bisa yadda aka bayar a rahoton.

Kalli hoto a kasa;

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa Kungiyar Ci gaban Addinin Musulunci ta Najeriya (IMN) da aka fi sani da ‘Yan Shi’a sun gargadi Gwamnatin Tarayya da cewa kada su kara jinkiri ko kuma kaisu ga fusata akan rashin sake shugaban kungiyar su, Sheik Ibrahim El-Zakzaky.

Kungiyar ta gabatar da gargadin ne ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya a ranar Talata da ta gabata, a yayin da suke taya El-Zakzaky murna na kai ga shekaru 68 da haifuwa, da kuma bacin ran cewa shugaban ya kai ga tsawon kwanaki 1,224 a kulle nan cikin birnin Abuja.

A bayanin shugaban kungiyar ‘yan Shi’a ta Jihar Sokoto, Sheikh Sidi Munnir, da manema labarai, yayi barazanar cewa kungiyar zata dauki sabon salo idan har Gwamnatin Tarayya ta ki sakin shugaban su.