Uncategorized
Allah Sarki! Wasu Mutane bakwai sun kuri Mutuwa a wata Gobarar Wutan Motar Tanki
Kimanin mutane bakwai suka kuri bakoncin mutuwa a wata gobarar wuta da ya auku a sakamakon fashewar Motar Tanki da ke dauke da Gas.
Naija News Hausa ta karbi rahoton wata Motar Tanki da ke dauke da Gas da ya Fashe da Wuta ranar Litini da ta gabata. An bayyana da cewa abin ya faru ne a wata gidan sayar da Man Fetur na Bolek a Jihar Kogi da ke fuskantar Babban Makarantar Jami’a na ‘Benue State University College of Health Sciences a garin Makurdi, babban birnin Jihar Benue.
Bisa ga bincike da ganewa manema labarai, Mutum bakwai ne suka kuri mutuwa a wannan gobarar wutan, biyu daga cikin su ma’aikata ne a gidan sayar da Man Fetur din, inda abin ya faru, Biyu kuma ‘yan Makarantan Jami’ar ‘Benue State University (BSU)’ ne, sauran mutane Ukkun kuma Kwastomomi ne da suka isa wajen don sayan Mai.
Ko da shike ba wanda ya mutu, amma akwai sani da cewa sun samu raunuka da daman a hadarin Motar Tankin da ya dauke da wuta.
Manajan Gidan Man, Mista John Ekpo ya bayyana ga manema labarai da cewa abin ya faru ne a missalin karfe Shidda (6:00 p.m) na Maraicen ranar Litini bayan da Motar Tankin ta gama saukar da Man da ta iso da ita a gidan Man.
“Motar Tankin na kokarin ya juya ne da fita daga cikin gidan Man a lokacin da kawai ta fashe a cikin gidan man da barin mutane da raunuka.” inji Mista Ekpo.
A halin yanzu suna asibitin Benue State University Teaching Hospital (BSUTH), Makurdi, inda ake basu kulawa ta gaske.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Gobarar Wuta ya kame wata Tiransifoma a birnin Abuja