Labaran Najeriya
Osibanjo na taron Bankwana da Hukumar NEC hade da Gwamnonin Najeriya
A yau Alhamis, 23 ga watan Mayu 2019, Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo na jagorancin zaman tattaunawa na bankwana da Kungiyar NEC, hade da Gwamnonin kasar.
Hidimar ya samu halartan kusan dukan Gwamnonin Jihohin kasar Najeriya a jagorancin Osinbajo, mataimakin shugaban kasa.
Naija News Hausa ta fahimta da cewa tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, ya samu halartan taron.
Bisa binciken tarihi, akwai sani da cewa kungiyar NEC, tsakanin shekarar 2015 har zuwa shekarar 2019 ta samu zaman tattaunawa ne sau 38, da kuma iya kafa baki ga kadamarwa 173 a kasar.
Mun sanar a Naija News Hausa a baya da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman bankwana da Kwamitin Dattijan Tarayyar Najeriya,
Tattaunawar ya fara ne bayan isowar shugaban kasa missalin karfe goma sha daya na safiya, anan gidan Majalisar Jiha da ke a fadar shugaban kasa, Abuja.
KARANTA WANNAN KUMA; Atiku zai ci Nasara da Buhari a Kotun Neman Yanci – PDP