Connect with us

Labaran Najeriya

Kalli dalilin da ya sa ba za a yi Hidimar Sallar Durbar ta shekarar 2019 a Jihar Katsina

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kwamitin Sarauta na Jihar Katsina sun gabatar da cewa ba za a yi hidimar Durbar ba a wannan shekarar a Jihar Kastine.

Ka tuna cewa mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari, a makon da ta gabata ya gabatar da dakatar da duk wata hidima a Jihar musanman ranar 29 ga Watan Mayu da za a rantsar da shugabannai a kasar.

A ranar Jumma’a da ta wuce, Magatakardan Kwamitin Nadin Sarauta a Jihar Katsina, Bello Ifo ya bayyana cewa lallai ba za a gudanar da hidimar Durban ba a wannan Sallah ta bana, dalilin kuwa itace don matsalar hare-hare da ake kaiwa a Jihar a ko yaushe.

Ya kara tunar da mutane ga harin da aka yi ba da jimawa ba a kananan hukumomin Batsari, Dan Musa, Kankara da  Wagini.

Naija News Hausa ta fahimta cewa a wannan shekarar, Jihar Katsina na daya daga cikin Jihohin kasar Najeriya da ta fuskanci ta’addanci da hare-haren ‘yan hari da makami a Jihar.

Haka kazalika aka sace surukin Gwamna Aminu Masari’ a watan baya a Jihar.

“Maimakon hidimar Sallar Durbar, za a gudanar da hidimar yin addu’a a Jihar don neman fuskar Allah da magance matsalar hare-hare da ke aukuwa a Jihar” inji Bello.

Mista Bello ya karshe da  bayyana cewa a bana ba za a gudanar da hidimar Sallar Durbar ba kamar yadda aka saba a kowace shekara a Jihar. “Maimakon hakan, za a bayar da ranar don jinya da ta’aziyya ga Iyalan da suka rasa ‘yan uwansu ga kowace hari a Jihar”.

Ka tuna da cewa Shugaba Muhammadu Buhari dan asalin Daura ne a Jihar Katsina.

KARANTA WANNAN KUMA;