Connect with us

Uncategorized

Karanta dalilin da yasa Joshua ya kashe makwabcinsa a garin Zazzaga, Jihar Neja

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Jami’an tsaron sun kame wani matashi mai shekaru 23, John Joshua, mazaunin garin Zazzaga dake a karamar hukumar Munya na Jihar Neja, da zargin kashe makwabcinsa.
Maneman labaran NewTelegraph sun ruwaito cewa Joshua ya soke makwabcin sa Yohanna Ali ne da yuka akan rashin fahimta da yarjejeniya da ya auku tsakanin marigayi Yohanna da mahaifinsa, Umar Parage da ke zaune a Zazzaga.
Jami’an tsaron da ke a rukunin hukumar tsaro ta Sarkin-Pawa ne suka ci nasara da kame Joshua bayan da suka karbi kirar kula daga mazauna.
Mahaifin marigayin ya fada a baya cewa yana da rashin fahimta tare da mahaifinsa wanda ake zargin, tun ranar 24 ga watan Mayu, wanda wani maƙwabcinsa ya shirya su tun a lokacin.
Joshua da ya ji da batun fadar da ke tsakanin mahaifinsa da Ali, sai ya hare shi da yuka ya kuma cacake shi har ga mutuwa.
Bincike ta nuna da cewa Joshua ya kashe Ali ne da akan cewa Ali na munsayar furci da mahaifinsa, wanda a fadin sa renin wayo ne daga marigayin ga mahaifinsa.
Kakakin yada yawun Jami’an tsaron yankin, PPRO Mohammed Abubakar ya bayyana da cewa lallai mai laifin kisan ya riga ya amince da zargin da ake na kisa a gareshi, da cewa kuma zasu mikar da shi a gaban kotu bayan bincike.
KARANTA WANNAN KUMA; Mutane 3 sun Mutu a sabuwar harin Mahara da Bindiga a kauyan Unguwar Rimi, Jihar Kaduna.