Connect with us

Uncategorized

Rundunar Sojojin Operation Hadarin Daji sun kashe ‘Yan Fashi 29 a Zamfara

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rukunin Sojojin Najeriya ta Operation Hadarin Daji sun kai wata mummunan hari ga ‘yan fashi da ke a gandun dajin Moriki na Jihar Zamfara.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa kimanin ‘yan fashi 29 sojojin suka kashe a ganawar wutan.

A ganewar wannan gidan labaran tamu, Sojoji biyu da dan sanda daya aka kashe a harin.

An sanar da lamarin ne a jiya Alhamis ga manema labarai daga bakin Kakakin yada yawun rundunar sojojin, Lt. Oni Orisun a Gusau.

A cewarsa, sojojin sun kaddamar da harin ne ga ‘yan fashi bayan da suka kauracewa sakon umurnin na bukatar suyi saranda cikin sa’o’i 24 da Kwamandan rundunar sojojin, Maj. Janar Jide Ogunlade ya ba su.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya cewa Boko Haram sun kashe mutane 20 a sabuwar hari da suka kai Ngamgam, Borno.

Bisa rahoton da aka bayar ga manema labarai, ‘yan ta’addan Boko Haram sun kai hari a shiyar Ngamgam, kilomita 50km ga Damasak, a nan karamar hukumar Mobbar, inda suka kashe akalla mutane 20.