Connect with us

Uncategorized

IMN: Majalisar Dokoki sunyi Alkawarin kafa baki ga neman a saki El-Zakzaky daga Fursuna

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A ranar Alhamis da ta gabata, Majalisar Dattijai ta Najeriya sun yi alkawarin cewa zasu tattauna da sauran mamban Majalisar da hukumar tsaro don neman a saki shugaban Kungiyar Ci gaban Musulunci (IMN) da aka fi sani da ‘Yan Shi’a, Ibrahim El-Zakzaky da Matarsa da hukumar tsaron DSS suka saka a fursuna tun shekarun baya da ta suka shige.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa hukumar DSS tare da hadin kan Gwamnatin Tarayya, ta kame El-Zakzaky ne tun shekarun baya da zargin jagoran halin kisa da tada tanzoma a kasa.

Jagoran babban rukunin Majalisar, Ado Doguwa, yayi alkawari ga ‘yan kungiyar Shi’a ne a lokacin da suka hari kofar gidan Majalisa da zanga-zanga.

“nayi alkawarin cewa zan gabatar da wannan zancen da bukatar ku ga Majalisa, zan kuma tabbatar da cewa an dauki mataki ta musanman ga sakin shugaban kungiyar ku da matarsa” inji Doguwa.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Kungiyar ci gaban Addinin Musulunci ta Najeriya (IMN) da aka fi sani da ‘Yan Shi’a sun yi barazanar cewa zasu taka rawar gani idan Gwamnatin Tarayya taki sakin Sheik Ibrahim El-Zakzaky da Matarsa.

Doguwa a bayanin sa ya kara da cewa ”Wannan majalisar inda zaka iya zuwa ne ka zuba yawun ka da abinda ke ci maka tuwo a kwarya”

“Ina tabbatar maku da cewa zan gabatar da zancen ga Majalisa, dukan mu kuma zamu tattauna da neman yanci ga shugaban ku”

”Don haka, zan karbi lambar wayan shugabannan kungiya ku. A duk lokacin da kuma na karbi hadin kan ‘yan Majalisa duka da Manyan a shugabancin kasar, zan mayar maku da martani don daukan mataki ta gaba” inji shi.

Kakakin yada yawun Kungiyar ‘Yan Shi’a, Ibrahim Musa, ya nuna damuwar sa da cewa lallai shugaban su ya kasa ga lafiyar jiki, sabili da hakan, ya kamata a sake shi don bashi kulawa da ta dace.

Ka tuna mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Daktoci da aka kawo daga kasar waje don binciken lafiyar jikin shugaban ‘yan shi’a, sun gabatar da cewa ya zama dole su tafi da shugaba Kungiyar ‘Yan Shi’a (IMN), Ibraheem El-Zakzaky da Uwar gidansa a kasar Turai don bashi kulawa ta gaske a yayin da lafiyar jikunansu ya kasa.