Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 31 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 31 ga Watan Yuli, 2019
1. Majalisar Dattijai ta Tabbatar da Duk Ministoci 43 da Buhari ya mikar da sunan su
Majalisar dattijan Najeriya ta tabbatar da nadin dukkan ministocin 43 da shugaba Muhammadu Buhari ya mikar da ita ga majalisar a kwanar baya.
Wannan ya biyo ne bayan cikar tsawon kwanaki biyar da Majalisar ke tantance jerin sunayan da shugaba Buhari ya bayar.
2. Shugaba Buhari ya bayar da takardun shaida ga Kotun Shugaban Kasa
A ranar Talata da ta gabata, shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da takardu 26 a yayin da yake zancen dage ga nasarar sa bisa hidimar zaben shugaban kasa ta 2019.
Naija News Hausa ta fahimta da cewa takaddun sun kunshi kwafin takardun shaidar sa na ilimi, wanda ya kunshi tabbataccen kwafi (CTC) na Takaddar Sakamakon jarabawawr Jami’ar Cambridge.
3. Lawan Ya Bayyana Shugabannin Kwamitin Majalisar Dattawa
Shugaban Majalisar Dattawa na Najeriy, Ahmad Lawan a ranar Talata, 30 ga Yuli ya ba da sanarwar shugabannin majalissar dattawa ta tara (9).
Ya sanar da hakan ne yayin zaman majalissar kafin Sanatocin su ci gaba da hutunsu ta shekara da shekara da aka daga zuwa ranar 24 ga Satumbar, 2019.
4. Majalisar Dattijai Ta Ba da Umarni ta musanman ga Obaseki Kan Rikicin Majalisar Edo
Majalisar dattijai a ranar Talata ta umarci gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da ya fitar da wata sabon sanarwa domin rantsar da ”yan majalisar dokokin jihar.
Naija News Hausa ta fahimta da cewa akwai matsaloli da majalisa jihar ke fuskanta akan jagorancin jihar.
5. Kotun Koli ta gabatar da ranar sauraron karar da Atiku yayi wa INEC
Kotun koli ta tsayar da ranar 20 ga watan Agusta, 2019, don sauraron karar da jam’iyyar PDP, babban jam’iyyar adawa ta Najeriya da dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, akan kalubalantar zaben watan Fabrairu.
Naija News ta tuno da cewa tsohon Mataimakin Shugaban kasa da dan takaran kujerar shugaban kasar a baya y bukaci hukumar INEC da binciken na”urar da aka yi amfani da ita a zabe baya.
6. Kotun Koli ta kori memba a Majalisar Wakilai ta Tarayyar APC
A ranar Talata da ta wuce, Kotun koli ta tsige Mustapha Usman, dan majalisar wakilai da ke wakiltar mazabar Yola ta Kudu da Yola ta Arewa a Tarayyar Girei na jihar Adamawa.
Naija News ta gane da cewa Usman ya wakilci mazabarsa a karkashin Jam’iyyar APC a gidan majalisa.
7. Majalisar dattijai ta dage sauraron karar har zuwa ranar 24 ga Satumba
Majalisar dattijan Najeriya a ranar Talata sun fara hutunsu na shekara da shekara bayan tantance sunayen ministocin da Shugaba Muhammadu Buhari ya mikar a garesu.
Ka tuna da cewa a baya Shugaba Buhari ya aikar da jerin sunayen mutane 43 don tantacewa da gabatar da su a matsayin Ministoci a kasar.
8. Gwamnatin Tarayya ta hana ‘yan Kungiyar IMN (Shi’a) da yin ayukan su a kasar
Gwamnatin tarayyar Najeriya a jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta sanarwar da hana Kungiyar Harkar Musulunci ta Najeriya (IMN), da aka fi sani da ‘yan Shi’a da tafiyar da ayukan su, musanman zanga-zanga.
Naija News Hausa ta gane da hakan ne bisa sanarwan da shugaban Jami’an tsaron ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya bayar a wata ganawa da manema labarai a birnin Abuja, ranar Talata da ta wuce.
Ka sami kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin NaijaNews.Com