Uncategorized
Shaidan ne ya shige ni – inji Mutumin da aka kama da laifin Jima’i da Almajirai 32 a Kontagora, jihar Neja
Rundunar Tsaron ‘yan sanda ta Jihar Neja ta sanar da kama wani mutumi mai tsawon shekarun haifuwa 33 da laifin lalata da Almajirai 32 a wata makarantar Almajirai da ke a Kontagora, wata karamar hukuma a jihar Neja.
Bisa rahoton da aka bayar ga manema labarai, an gane Malam Abdullahi Abubakar ne da yin lalata da daliban wata makarantar almajirai a unguwar Sabon-Gari ta yankin Kontagora.
An iya bayyana da cewa Abdullahi, wanda ya zan daya daga cikin masu kula da daliban, ya kan cire wa daliban wandunan su ne a yayin da suke bacci, sai kuwa yayi lalata da su.
Bisa fahimtar Naija News Hausa akan rahoton, akwai ganewa da cewa mutumin ya dade da yake hakan ga daliban da ke Almajiranci a shiyar.
An sanar da rahoton ne a farko ga ‘Yan Sanda daga bakin Kwamandan ‘yan HISBAH ta yankin Kontagora, Malam Murtala Abdullahi, tun ranar 22 ga Watan Yuli 2019 da ta gabata. A bayan hakan ne rukukin Jami’an tsaron ‘A’ Division ta Kontagora suka bi likin Malam Abdullahi har suka kuwa kama shi.
Ga bayanin Malam Murtala a kasa bayan da aka kama shi;
“Ba zan iya bayar da bayani a yadda na fara yin lalata da ɗaliban nan ba; a gaskiya wannan aikin shaidan ne,” in ji Abdullahi a yayin da yake zantawa manema labaran Arewa City News.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar Neja, Mohammad Abubakar ya bada tabbacin lamarin.
“Rukunin Tsaron mu zata bi tushen wannan lamarin har ma da gano wadanda ke boyo da sunan makarantan almajiri don aikata irin wannan lalata da dalibai. Ba kuwa tare da jinkirta ba, hukumar tsaro zata tabbatar da maganin su” inji Mohammad.
Ya kuwa kare da cewa lalai hukumar su zata tabbatar da mikar da Abdullahi a gaban Kotu don hukunci bayan bincike.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa ‘Yan Sandan Jihar Neja sun kame Matasa Uku da zargin yiwa ‘yar shekara 14 Fyaden Dole