Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 18 ga Watan Satunba, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 18 ga Watan Satunba, 2019
1. Shugaba Buhari ya Rushe SPIP din Obono-Obla
Shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari ya rushe kwamitin Binciken Shugaban Kasa na Musamman wanada Okoi Obono-Obla ya jagoranta kan Maido da kadarorin Jama’a (SPIP).
Naija News ta ruwaito cewa mai ba da shawara na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya bayar a ranar Talata, 17 ga Satumba da ta gabata.
2. Rundunar Sojojin Najeriya ta fara yin Garkuwa ga Janar akan Miliyan Sama da N400m
An fara Shari’a da binciken tsohon Kwamandan Rundunar Sojoji (GOC) 7 Division, Sakkwato, Maj.-Gen. Hakeem Otiki, bisa zargin satar da ya kai miliyan N400.
A cewar babban hafsan sojojin, Laftanar-Janar. Tukur Buratai, yayin da yake kaddamar da Babbar Kotun Martial ranar Talata a Abuja, ya ce shari’ar ta yi hannun riga da Dokokin Rundunar Soja ta Armed Forces Act Cap A20 ta shekarar 2014.
3. INEC ta Bayyana Damuwarta kan Rikici gabadin Zaben Jihar Kogi
Hukumar gudanar da Zaben Kasa, INEC ta jihar Kogi ta nuna damuwar ta game da yiwuwar tashin hankali yayin da zaben gwamnoni na ranar 16 ga Nuwamba na gabatowa.
Naija News ta fahimci cewa Kwamishinan Zabe na mazaba (REC) a Kogi, Farfesa James Apam, a ranar Talata ya bayyana wannan ne a wurin bayyana “fita da jefa kuri’a (GOTV), Ilimin masu jefa ƙuri’a da kuma dakatar da cin zarafin mata a siyasa (STOP VAWIP)” da aka yi a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.
4. Xenophobia: South Afirka Ta Ba da Izinin Saukar Jirgin Sama ga Kamfanin Jirgi ta Air Peace
A ranar Talata da ta wuce ne hukumomin South Afirka suka baiwa kamfanin jirgin Sama ta Air Peace, watau kamfanin jirgin saman a Najeriya, izinin saukar da jirgin nasa a kasar.
Naija News ta fahimci cewa an ba da izinin ne don ba da damar daukar wasu ‘yan Najeriya 320 da ke shirye da su koma kasar Najeriya sakamakon munanan hare-hare da ke faruwa musamman kan ‘yan Najeriya a kasar South Afirka.
5. Gwamnan jihar Kwara ya nada Matashiya mai shekaru 26 a matsayin Kwamishina
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara, ya nada Miss Joana Nnazua Kolo, mace mai shekaru 26 da haihuwa da ke hidimar bautar kasar (NYSC), a matsayin kwamishina.
Naija News ta ba da rahoton cewa Matashiyar mai shekaru 26 na daga cikin kwamishinoni mata hudu wadanda aka zaba da mika sunayensu ga majalisar dokokin jihar Kwara a ranar Talata, 17 ga Satumbar.
6. Shugaba Buhari ya fadawa Hukumar ‘Yan Sanda Abinda zata yi da Rundunar Tsaron Najeriya
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya tuhumi membobin Hukumar ‘Yan Sanda da su kara kokarinsu wajen tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ta gudanar da ayukan ta yadda ya kamata.
Da shugaba Buhari ke magana a ranar Talata a Abuja yayin karbar rahoton shekarar 2018 na Hukumar, ya ce, “Hukumar na da mafi wahala da tsanantaciyar ayuka ta musanman akan tsaro a kasar.”
7. Gwamnatin jihar Ekiti ta rike da bashin Albashin Ma’aikata na kimanin kudi Biliyan N57bn – Fayemi
Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya bayyana cewa jihar ta mallaki bashin albashin ma’aikata a aikin farar hula da suka kai akalla Naira biliyan hamsin da bakwai (N57bn).
Gwamna Fayemi ya zargi gwamnatin da ta gabata a jihar kan lamarin, ya bayyana cewa rashin biyan albashi da alawus din da gwamnatin Fayose ta saba yi ya haifar da hakan.
8. Kungiyar ECOWAS Ta Roki Buhari Don Sake Bude Bodar Kasar
Majalisar ECOWAS ta roki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da ta bude katangewar da aka yi wa bodar kasar Najeriya.
Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa, majalisar ta bayyana cewa, bodar da aka katange ya haifar da rashin kasuwanci da gudanarwa ga a yankunan da ECOWAS ta mallaka.
Karanta kari da cikakkun Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com