Connect with us

Uncategorized

INEC: Sakamakon Zaben Jihar Kogi kamin INEC ta Dakatar da Kirga ranar Lahadi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar INEC ta Dakatar da Kirgan Sakamakon Zaben Jihar Kogi

Hukumar Gudanar da Hidimar Zabeb Kasa (INEC) ta Jihar Kogi a ranar Lahadi ta sanar da cewa ta dakatar da sanarwar sakamakon zaben ranar Asabar, 16 ga Nuwamba na zaben gwamna a jihar Kogi.

Wannan sanarwan an bayar da ita ne a bakin Babban Ofisan da Shugaban Hukumar INEC ta Jihar, wanda ke jagorancin hidimar zaben.

Jami’in, yayin da yake ba da dalilai game da dakatarwar da kuma jinkirtawa ya lura cewa yayi hakan ne saboda sakamakon kananan hukumomi biyu da suka saura basu rigaya sun iso dakin kirga ba.

Ko da shike dai ya sanar da cewa zasu ci gaba da kiirgan a ranar Litini, 18 ga watan Nuwamba, watau a Yau.

Naija News Hausa ta kula da cewa a daidai lokacin da aka dakatar da kirgan, Dan takara daga Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Yahaya Bello na gaban Musa Wada, Dan takaran Peoples Democratic Party (PDP) da yawar kuri’u a tseren gwamnan Jihar Kogi.

Kamar yadda INEC ta sanar a rahotannai, Gwamna Bello na APC na da kimilar kuri’u 184,430 yayin shi Wada da PDP ke da yawar kuri’u 176,803.