Connect with us

Labaran Najeriya

Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Ya Cika Shekaru 62, Ga Sakon Shugaba Buhari Zuwa Gareshi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaba Buhari ya taya tsohon shugaban kasa Jonathan murnar cikar sa shekaru 62 da haihuwa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan murna a cikar shekara 62 ga haihuwarsa ta.

Buhari ya taya Jonathan murna ne ta hanyar hada kai da ‘yan kasar da yin addu’o’in tsawon rai, lafiya da kuma karin karfin gwiwa don ci gaba da yiwa kasa hidima.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayin wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Mista Femi Adesina bayar. Da cewa yana farin ciki da dangi, abokan arziki da abokan siyasa na tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan. Yana mai yaba masa kan kyawawan shawarwari ga shugabannin ciki da kasashen wajen Najeriya tun bayan da barin ofis, da kuma rabar da kwarewarsa ta yin aiki a matakai daban-daban na gudanar da mulki.

Shugaba Buhari ya yi imanin cewa halin kaskantar da kai da kishin kasa da tsohon Shugaban kasar ke da shi zai ci gaba da yaduwa a fadin kasar, tare da fadakar da al’ummomi da za su zo kan sadaukarwar musanman don dorewar dimokiradiyya da kuma samar da ci gaba mai dadewa a kasar.

Daga nan Shugaban kasar yayi fatan tsawon shekaru cike da murna ga Iyalan tsohon Shugaban.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, yayin da yake magana kan halin da Najeriya ke ciki, ya bayyana cewa idan har Annabi Isa zai kasance a wannan kasar a wannan lokacin, zai yi korafi kan yadda masu iko ke tafiyar da mulkin kasar.

Tsohon Shugaban a cikin sanarwar sa ya karfafa malaman adinin Kirista da cewa kada su yi shuru game da abin da ke faruwa a kasar amma a koyaushe su fadi gaskiya ga mutanen da ke kan mulki.