Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis 10, ga Watan Janairu, a Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis 10 ga Watan Janairu, 2019
1. Shugaba Buhari ya kaddamar da kwamiti na fasaha akan sabon tsarin albashi
Shugaba Muhamamdu Buhari ya kafa kwamitin shawarwari na fasaha don aiwatar da tsarin sabon albashi na kasa, kuma ya sake nuna goyon bayan sa ga wannan tsarin.
Shugaban ya bayyana goyon bayansa akan wannan shirin ne a yayin da yake gabatar da kwamitin a baya a gaban taron majalisar Tarayyar Tarayya (FEC),da cewa “Lokaci ya yi ne don aiwatar da wannan shiri”.
2. Hukumar EFCC ta kame wani mutum tare da kudi $207,000 a filin jirgin saman ta Kano
Hukumar EFCC ta kame wani mai suna Sani Abdullahi a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.
Hukumar EFCC ta kame Sani ne a lokacin da ake binciken fasinjoji da ke shiga jirgin saman kasar China da ga nan Kano, sun ka me shi ne don ya ki bayyana matsayin kudin da ya ke dauke da shi na kimanin dala 207,000 (Miliyan 63,135,000) a fasarar kudin Najeriya.
3. Hukumar INEC ta ce babu watsar da sakamakon zaben 2019 a na’ura ko ga wata hanyar sadarwa
‘Yan kwanaki kadan da shiga zaben tarayya ta shekarar 2019, Hukumar INEC ta ce hukumar za ta gabatar da rahoton zaben tarayyar ne kawai bayan an kamala dukan zabe.
Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana wannan ne cikin jawabinsa a gabatarwar taron hukumar da suka yi a ranar Talata tare da manema labarai a birnin Abuja.
4. Atiku na kular hankali kuma amintacce ne, Jam’iyyar PDP sun gayawa Tinubu
‘Yan Jam’iyyar PDP da ke gudanar da shirin zaben 2019 sun mayar da martani ga Bola Tinubu, shugaban Jam’iyyar APC na tarayya akan zargi da kuma fade-faden sa game da Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa ta Jam’iyyar PDP.
Kalaman daga bakin kakakin Jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan a cikin wata sanarwa na kamar haka, “A matsayin ka na babban shugaba na kasar Yarbawa, ka yi kula da kuma amfani da karin maganar yarbawa da ke cewa “Idan an aiki karamin yaro da sakon bauta, ya kan aiwatar da sakon ne da hankalin sa” in ji kalmar Kola zuwa ga Tinubu.
5. Ba zan gudanar da neman zabe na ba da tattalin arzikin kasar – inji Buhari
Shugaban kasar, Muhammadu Buhari a ranar Laraba da ta gabata ya ce ba zani gudanar da shirin neman zabe na ba da tattalin arzikin kasar kaman yadda gwamnatin da ta saba yi.
6. Boko Haram: Sojoji a da sun kulle babbar hanyar Maiduguri, amma a halin yanzu sun sake bude hanyar
Sojoin Najeriya sun kulle babban Hanyar da ta bi Maiduguri zuwa Damaturu da hanyar da ta bi Damaturu zuwa Potiskum a jihohi Borno da Yobe a ranar Laraba da ta wuce.
A halin yanzu an sake bude hanyar ga jama’a da kuma hukumomin, da cewa an kulle hanyar ne daman don tabbatar da tsaro da kuma dakatar da ayukan kungiyar Boko Haram daga yankin.
7. Gwamnatin tarayya ta gabatar da ranar 23 ga watan Janairu don aikawa hukumar NASS takardan sabon tsarin albashin ma’aikata
Ganin irin barazanar Kungiyar Ma’aikata da Tarraya da wasu hukumomi da ke kasar, Gwamnatin tarayya ta gabatar a ranar Talata da cewa za ta aika da takardan tsarin albashin ga NASS a ranar 23 ga watan Janairu.
Wannan ya bayyana ne bayan jerin tattaunawa tsakanin gwamnatin tarraya da shugabannin kungiyar ma’aikata a zama ta karshe da suka yi.
8. ‘Yan sanda sun bayyana nemar kama wani shugaban ‘yan Yuniyan (NURTW) akan farmaki da aka kai wa APC a Jihar Legas
Jami’an tsaron ‘Yan sandan Jihar Legas sun gabatar da neman kame wani mai suna Mustapha Adekunle da aka fi saninsa da suna ‘Segio’ akan aiwatar da tashin hankali da farmaki da ta auku a taron ‘yan ‘Jam’iyyar APC da aka yi a ranar Talata da ta gabata.
Seigo wani memba ne na Kungiyar ‘yan yuniyan (NURTW), wanda a ke zargin sa da jagoran tashin hankali da farmaki da ta faru a taron Jam’iyyar APC a ranar talata.
9. Nnamdi Kanu ya yi magana akan hirar Buhari da masu yada labaran ‘Arise TV’
Shugaban kungiyar Biafra (IPOB), watau Nnamdi Kanu ya sauta wa Shugaba Muhammadu Buhari da cewa shugaban bai gabatar da yankunan aikin kasar yadda ya kamata ba a wajen hirar da shugaban yayi da kamfanin watsa labaran talabijin na ‘Arise TV.
‘Kamfanin watsa labaran ‘Naija News’ ta ruwaito da cewa shugaba Muhammadu Buhari na wata hira da kamfanin watsa labaran ‘Arise TV’ inda shugaban ke amsawa zargin da ake yi masa akan cewa bai bada kulawa isasshe ba ga yankin Iyamiran kasan wajen sanya shugabannan jagorancin kasar.
10. Jeff Bezos da matar sa na shirin rabuwar aure bayan shekaru 25 da suke tare
Jeff Bezos mafi kudi a girman duniya gaba daya wanda ke da kamfanin kasuwanci na Amazon ya zo ga yarjejeniya da matarsa MacKenzie Bezos don rabuwar bayan shekaru 25 da suka yi aure.
Mutum mai shekaru 54 da haihuwa, da kuma mafi arziki a duniya kamar yadda kamfanin Billionaire ta Bloomberg suka bayar da cewa yana da kudi kimanin $137bn. Mutumin ya sanar da wannan ne a kan yanar gizon twitter na sa.
Samu cikakun labarai da ga Naija News Hausa