Labaran Najeriya
APC/Kannywood: ‘Yan wasa Fim na Hausa sun marawa shugaba Buhari baya a Jihar Kano
Kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa a ranar jiya da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya sauka daga jirgin sama a Jihar Kano don kadamar da hidiman yakin neman sake zaben sa.
Rahoto ta bayar da cewa ‘yan wasan fim din sun mamaye wajen hidimar don marawa shugaba Muhammadu Buhari baya da Jam’iyyar APC ga zaben tarayya da ta gabato.
Hidimar ta samu halartar wasu kwararun yan wasan Kannywoord kamar, Ali Nuhu, Zainab Booth, Sadik Sani, Rukayya Dawayya, Baba Ari da Rabiu Daushe.
Hidimar da aka gudanar a filin wasan kwallon Sani Abacha da ke a Jihar Kano a ranar Alhamis da ta gabata don hidimar yakin neman zabe ga shugaba Muhammadu Buhari da Jam’iyyar APC gaba daya.
An kuma iya gano shahararun mawakan Kannywood kamar su Ado Gwanja, Ibrahim Yala da kuma Rarara Kahutu a wajen hidimar.
Baba Ari da Rabiu Daushe sun taka irin nasu rawar gani kuma a yayin da suka fada wa rawa a filin taron da bawa jama’ar da ke wajen dariya.
Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Rikici ya barke tsakanin ‘yan shirin Fim na Kannywood, a yayin da Ummi Ibrahim (ZeeZee) da Zaharaddeen Sani suka yi barazanar kai karar junan su akan kudi da Jam’iyyar PDP ta ba su a wata ganuwa da suka yi a Jihar Kaduna, a jagorancin Sanata Bukola Saraki.
Karanta kuma: Ban damu ba ko da na fadi ga zabe na gaba – inji El-Rufai, Gwamnan Jihar Kaduna