Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 12 ga Watan Fabrairun, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 12 ga Watan Fabrairun, 2019

 

1. Kada ku kunyartar da ni, Gwamna Amosun ya roki mutanen sa a ralin shugaba Buhari a Jihar Ogun

Gwamnar Jihar Ogun, Ibikunle Amosun ya roki jama’ar Jihar sa da dakatar da halin banza da ta’addanci da suka nuna, watau yin jifar duste a yayin da ake hidimar ralin Jam’iyyar APC ta jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ga neman sake zabe da aka gudanar a filin kwalon kafa na MKO Abiola a nan Jihar.

Tanzomar ta fara ne a yayin da aka marabci Oshiomhole don gabatarwa. Daga fara magana sai ‘yan ta’adda da ke wurin suka fara masa tsuwa, daga nan suka fara kokarin jifar sa, kokarin yin hakan sai jifar dutsin ya nufi inda shugaba Muhammadu Buhari ya ke, amma dai Jami’an tsaro da ke a wajen ba su bari dutsin ya fada ga jikin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba.

2. Jam’iyyar APC na shirin sayar kuri’u Miliyan 15m da kudi kimanin Biliyan N112.5b a zaben ranar Asabar – PDP

‘Yan Jam’iyyar PDP da ke a Jihar Ekiti, sun zargi Jam’iyyar APC da shirin yin makirci na sayan kuri’u ga zaben shugaban kasa da za’a yi a ranar Asabar, da kuma zabe Gidan Majalisa da zai biyo baya.

“Jam’iyyar APC sun shirya kudi kimanin biliyan N112.5bn don sayan kuri’u Miliyan 15 daga jama’a, a farashin naira N7,500 daga kowane mutun daya.

“Akwai kuma shiri daga Jam’iyyar APC don tsananta wa hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) da shirya takardan sakamakon zabe guda biyu don kawo ruduwa ga sanar da ainihin sakamakon zabe 2019” inji PDP

3.  Hukumar DSS sun kame Ben Bako, Mai yada labarai ga Jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna

Hukumar sun kame Bako ne da zargin furci na tashin hankali da tada zama tsaye.

An kame Ben Bako ne sakamakon wata bidiyo da ke dauke da wata furcin tashin hankali da ya yi akan zaben 2019 a wajen hidimar ralin yakin neman zabe da Jam’iyyar ta yi a garin Kafanchan, karamar hukumar Jama’a ta Jihar Kaduna.

“Bayan tattaunawar da bincike da DSS suka yi wa Mista Ben, sai suka tafi da shi zuwa birnin Abuja ranar Lahadi da ta gabata” inji Mista Catoh.

4. Tsohon Sakataren NFF, Taiwo Ogunjobi ya Mutu

Tsohon sakataren Kungiyar ‘Yan Kwallon Najeriya, Mista Taiwo Ogunjobi ya mutu sakamakon wata rashin lafiya da yayi na ‘yan kwanaki.

Ko da shike ba a bayyana irin rashin lafiyar da Mista Taiwo yayi ba, amma mun sami tabbaci a Naija News da mutuwarsa.

5. Kungiyar NBA ta yi barazanar karar  Gwamnan Jihar Zamfara ga Kotun ICC

Kungiyar Alkalan Kasar Najeriya (NBA0 ta Jihar Zamfara sun yi barazanar karar Gwamna Abdulaziz Yari a gaban kotun hukunta manyan laifuffukan duniya (ICC), idan har ya ci gaba da bayar da shawarar tanzoma ko kauracewa zaben tarayya ta 2019.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa Gwamna Yari ya yi alwashin cewa zai rushe zaben Jihar idan har Hukumar INEC ta cire jam’iyyarsa ga tseren takara ga zaben 2019.

6. Biafra: Shugaban (IPOB), Nnamdi Kanu ya yi alkawarin ‘Hallaka’ Jubril na Sudan a ranar Alhamis

Shugaban kungiyar ‘yan asalin Biafra (IPOB), Mazi Nnamdi Kanu ya yi barazana da cewa a ranar Alhamis din nan, zai bayyana ga jama’a kuma zai halakar da Jubril na Sudan da ke nan cikin Aso Rock.

Ya fada da cewa, harwayau mutane basu yarda da bayyanin sa ba a kan Jubril daga Sudan da ke cikin Aso Rock.

7. Rundunar Sojojin Najeriya sun sanar da zabin sabbin Ofisoshi

Rundunar Sojojin Najeriya a ranar Lahadi, 10 ga Watan Fabrairun, shekara ta 2019 sun gabatar da sanya sabbin Manyan Ofisoshi a rundunar.
Daya daga cikin Manyan Jami’an Sojojin, Col. Aliyu Yusuf, Daraktan Yada Labarai ga Rundunar Sojojin ne ya bayyana hakan ga gidan labarai tamu na Naija News a jiya Litinin 11 ga Watan Fabrairun.

8. Hukumar INEC ta bayyana kimanin katunan zabe (PVS) da suka kama da wuta

Hukumar gudanar da zaben kasar Najeriya (INEC) sun gabatar da iyakan katunan zaben kasa da suka kama da wuta a Jihar Abia da Plateau.

INEC sun bayyana da cewa katuna 8,966 ne suka kone da wuta sakamakon kamun wuta da ya auku a Jihohin kasar biyu. Watau Jihar Abia da Jihar Plateau a cikin kwanaki bakwai da suka gabata.

9. Ralin shugaban kasa da aka yi a Jihar Ogun ta karshe da birkicewa

Hidimar ralin neman zaben shugaban kasa na Jam’iyyar APC da aka gudanar a Jihar Ogun ya karshe da birkicewa a yayin da aka fara jefe-jefen dutsi ga ‘yan takaran.

Hidimar da ta halarci, shugaba Muhammadu Buhari, Adam Oshiomole, Gwamnar Jihar Ogun, Ibikunle Amosun da shugaban Jam’iyyar APC, Bola Tinubu.

Ka sami cikkakun labaran Najeriya a shafin www.hausa.naijanews.com