Uncategorized
Mataimakin jagoran hidimar zabe na Jam’iyyar APC a Bauchi ya janye daga APC
Ana ‘yan kwanaki kadan da fara zaben kasar Najeriya ta shekarar 2019, wani sannan mamba na Jam’iyyar APC a Jihar Bauchi yayi murabus da Jam’iyyar.
Mataimakin shugaban Jam’iyyar APC ga yakin neman zabe, Lura Musulmi ya gabatar da cewa ya janye daga Jam’iyyar APC.
Musulmi, dake taimakon wakilci ga lamarin yakin neman zabe ga dan takara gidan majalisar wakilai, Dalhatu Abubakar Kantana a yankin kananan hukumomin Dass/Tafawa Balewa/Bogoro ta Jihar Bauchi, ya bayyana da cewa bai da muradin ci gabada zaman mamban jam’iyyar kuma.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa kimanin mutane 100,000 suka janye daga Jam’iyyar PDP zuwa APC a Jihar Sokoto.
Ko da shike dai, Musulmi bai bayyana dalilin da ya sa ya janye daga Jam’iyyar ba, amma ya gabatar da cewa shi ya janye daga Jam’iyyar kuma bai da muradin komawa ga wata Jam’iyya ba a halin yanzun nan.