Uncategorized
An sace Surukin Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari
‘Yan hari da makami sun sace Hajiya Hauwa Yusuf, surukin gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari, da safiyar ranar Jumma’a missalin karfe 3 na safiya a nan gidan ta da ke Dandume, Jihar Katsina.
Wasu ‘yan hari da makami da ba a gane da su ba sun hari gidan Hajiya Hauwa da ke da shekaru 80 da haifuwa, sun kuma wuce da ita inda ba wanda ya sani.
Naija News Hausa ta samu ganewa da cewa Hajiya Hauwa na zaman uwa ne ga Binta Masari, daya daga cikin mata ukku da gwamnan Jihar Katsina ya aura. kamar yada jaridar Daily Trust suka bayar.
Rahoto ta bayar da cewa ‘yan harin sun fada wa gidan ne da bakaken abu a fuskar su yadda ba wanda zai iya gane su.
Ko da shike ba cikkaken bayani a game da harin a lokacin da abin ya faru har zuwa yanzun nan. Amma dai an iya gane da cewa ‘yan harin sun yi wa mutanen gidan duka kwarai da gaske, sun kuma amshe na’urar sadarwan su duka yadda ba wanda zai iya aika kira ko neman taimako.
Ba mu samu wata rahoto ko bayyani ba tukuna daga jami’an tsaron jihar har yanzu. duk da kokarin da aka yi na samun furci daga shugaba jami’an tsaron ‘yan sandan Jihar, SP Gambo Isah.
Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa ‘yan hari da bindiga sun sace babban kocin kwallon kafa ta Najeriya da ke a Jihar Katsina.