Connect with us

Uncategorized

Gwamnan Jihar Neja ya kafa kwamiti don karfafa karfin wutan lantarkin Jihar

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Abubakar Sani Bello, Gwamnan Jihar Neja ya kafa wata kwamiti da za ta samar da mafita ga raguwa da kuma matsalar issashen karfin wutan lantarki da ake fuskanta a Jihar.

Gwamnan ya bayyana da cewa wutan tsawon awowi shidda (6Hrs) da hukumar Abuja Electricity Distribution Company (AEDC) ke bayar wa ga kananan hukumomin Jihar bai dace ba.

“Ban amince da wutan lantarki na awowi shidda da AEDC ke bayarwa ga Minna, babban birnin Jihar Neja da sauran kananan hukumomin Jihar ba” inji Gwamnan.

Kwamitin da Gwamnan ya kafa ya kunshi, Mataimakin sa ga kujerar Gwamna, Alhaji Ahmed Mohammed Ketso da Kwamishanan Kudi, Hon. Mallam Zakari Abubakar.

Gwamna Bello ya umurce su da ganawa da hukumar AEDC ta Abuja tsakanin nan da awowi 24 da kuma tabbatar da cewa an samu canji daga yadda ake bayar da wuta a garin Minna da sauran kananan hukumomi da ke kewaye da ita.

Ya kuma sanya Alhaji Ahmed Mohammed Ketso ga jagorancin kwamitin.

Naija News Hausa ta gane da cewa Jihar Neja na da Dam da kuma sanfarin dan dama da ke bayar da wutan lantarki ga kasar Najeriya, amma Jihar na kuma daya daga cikin Jihohin kasar da ke samun matsalar wuta.