Connect with us

Uncategorized

‘Yan Hari da makami sun sace Matan Alkali Sulaiman a Jihar Nasarawa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

‘Yan Hari da makami a Jihar Nasarawa sun hari Suleiman Abubakar, Ciyaman na Hukumar Alkalan kasar Najeriya ta Jihar Nasarawa (NUJ), sun kuma sace matarsa, Yahanasu Abubakar.

A bayanin Suleiman da kungiyar manema labaran Najeriya, ya bayyana da cewa abin ya faru ne missalin karfe bakwai na maraicen (7:00PM) ranar Laraba da ta gabata a da ta bi Gudi zuwa Garaku, a nan karamar hukumar Akwanga.

“Maharan sun harbi motar Hukumar mu da muke tafiya da ita daga shiyar Keffi a inda matar ta sa ta je don ta yi rajistan sunan ta ga hidimar bautar kasa (NYSC)” inji Sulaiman.

Ya kara da cewa motar su ta fada ga wata babban rami bayar da ‘yan harin suka harbi motar. “Da suka ga motar ta lakke a rami, a gaggauce sai suka haro motar da sace mata na, matar dan gidan majalisar Jihar da muka taimaka wa da dauka hade da wasu mata biyu da ke cikin wata mota da ke biye da mu kuma” inji shi.

Ofisan Jami’an ‘yan sandan yankin, ASP Samaila Usman, watau Kakakin yada yawun jami’an tsaron, ya bayyana da cewa hukumar su sun watsar da darukan tsaro a shiyar da abin ya faru don ribato rayukar matan da aka kame.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Wasu Mahara da Makami sun sace wani Firist na Ikklisiyar Katolika da ke a Jihar Kaduna.